Da Ɗumi-Ɗumi: A karo na biyu, Saudiyya ta kara wa'adin jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki

Da Ɗumi-Ɗumi: A karo na biyu, Saudiyya ta kara wa'adin jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki

  • Gwamnatin Saudiya ta kara lokacin jigilar maniyyata Hajjin bana 2022 zuwa ƙasa mai tsarki
  • Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa NAHCON ta ce wannan cigaban zai kwantar da hankulan maniyyata aƙalla 3,000 dake jiran tsammani
  • Hukumar ta ce tuni ta kammala duk wasu shirye-shirye na kwashe ragowar Maniyyata zuwa Saudiyya don sauke farali

Hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar Saudiyya (GACA) ta sanar da ƙara wa'adin Jigilar maniyyatan bana zuwa cikin ƙasa mai tsarki don gudanar aikin Hajji 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON ta ce wannan cigaban zai kwantar da hankulan maniyyatan Najeriya 3,000 waɗan da har yanzu suke dakon jirgin da zai kwashe su zuwa Saudiyya.

Saudiyya ta ƙara wa'adin jigilar maniyya
Da Ɗumi-Ɗumi: A karo na biyu, Saudiyya ta kara wa'adin jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Ta ƙara da cewa labarin farin cikin na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin Najeriya da gwamnatin Saudiyya bisa jagorancin shugaban NAHCON na ƙasa, Alh Zikrullah Hassan.

Kara karanta wannan

'Ba zata saɓu ba' Jam'iyyar APC ta tashi tsaye, ta fara shirin dakile sauya shekar wasu mambobinta zuwa PDP

Idan zaku iya tunawa shirye-shiryen Najeriya game da aikin Hajjin bana 2022 kewaye yake da kalubale kala daban-daban saboda rashin tsari mai kyau daga hukumar NAHCON da hukumomin jin daɗin Alhazai na jihohi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan ya haddasa zanga-zanga da kai ruwa rana tsakanin maniyyata waɗan da suka lale kuɗi suka biya tun shekara 2019 kafin Annobar Korona ta tsayar da komai cak.

NAHCON ta sake shirye-shiryen kwashe maniyyata

Bugu da ƙari a cikin sanarwan, NAHCON ta ce wannan cigaban ya bai wa kamfanonin sufurin jiragen sama biyu, Max Air da Azman Airline, cigaba da jigilar maniyyata daga inda suka tsaya.

The Nation ta rahoto wani sashin sanarwan ya ce:

"A halin yanzu hukuma ta kammala duk wasu shirye-shirye tare da kamfanin Sufurin Flynas domin aikin sawu uku na jigilar kwashe ragowar maniyyatan Kano da Abuja."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai wa Ayarin motocin shugaba Buhari hari a Katsina, sun jikkata mutane

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta fara kokarin hana guguwar sauya sheka ta yi awon gaba da Mambobinta a Kebbi

Alamu sun nuna uwar jam'iyyar APC ta tsoma baki domin shawo kan rikicin da ke kwashe mata 'ya'ya a jihar Kebbi.

Jam'iyya mai mulki ta kira taron masu ruwa da tsaki da mambobin da ran su ya ɓaci domin tattauna wa da kuma yin sulhu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262