Babu wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a cocin Anambra – ‘Yan sanda

Babu wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a cocin Anambra – ‘Yan sanda

  • Yansandan jihar Anambara sun karyata zargin da aka yiwa Fulani na kai wa cocin Grace na God hari a ranar Lahadi
  • Kwamsihinan yansandan jihar Anambara yayiwa mutanen da ke yada labaru karya a Facebook kashedi da su daina
  • Fusattatun matasa sun kona wani barawo da yayi yunkurin yiwa wani bawon Allah fashi a kusa da cocin Grace na God

Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta karyata rahoton da aka wallafa a Facebook cewa wasu Fulani hudu sun kutsa cikin cocin Awada Grace na God a ranar Lahadi da nufin tayar da bam a cocin kamar yada jaridar Daily Trust ta rawaito.

Hukumar yansanda a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya ta bakin kakakinta, DSP Ikenga Tochukwu, ta ce labarin kanzon kuregen da aka wallafa Facebook, an yi shine domin a haifar da tashin hankali da kiyayyar kabilanci da na addini a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

Ya bayyana rahoton a matsayin mugunta da abun takaici, ya ce, Jami’an su insa wurin sun yi tambayi wadanda abin ya faru a gaban su. Mun samu labarin cewa fusatattun mutane ne suka kona wani barawo yayi kokarin yi wani mutum fashi. Rahoton jaridar Premium Times

VANNM
Babu wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a cocin Anambra – ‘Yan sanda; FOTO VANGUARD
Asali: Facebook
"Wannan mummunan martani ne kawai da mai amfani da Facebook ya yi don cimma burinsa na son ta da zaune tsaye. Ku tuna a ko da yaushe rundunar ‘yan sandan ta na Allah wadai da matakin daukan doka a hannu da jama’a ke yi a duk lokacin da suka kama wadanda ake zargi da aikata wani laifi ba tare da neman ‘yan sanda sun gudanar da binciken da ya dace ba.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tochukwu ya ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Echeng Echeng, ya bayar da umarnin binciken wanda ya yada labarin karya a shafin Facebook tare da yiwa masu hali irin nashi gargadi da su daina yada labarum karya.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Rashin tsaro: Sarkin Katsina ya dakatar da Hawan Sallar Idi

A wani labarin, Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da hawan Daushe a lokacin bikin sallar Eid-el-Kabir da za a gudanar a ranar Asabar.

Rahoton Daily Nigeria Dakatawar ta fito ne a jawabin da mataimakin sakataren majalisar masarautar jiha, Sule Mamman-Dee ya fitar a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa