Gwana ta gwanaye: Mai hijabi ta girgiza intanet yayin da ta nuna kwarewa a kwallon kafa

Gwana ta gwanaye: Mai hijabi ta girgiza intanet yayin da ta nuna kwarewa a kwallon kafa

  • Wata kyakkyawar budurwa ta girgiza intanet bayan da ta nuna kwarewarta ta wasan kwallon kafa
  • Bidiyon yadda ta buga kwallon kafa kamar wata kwararriyar 'yar wasa a lokacin da take sanye da hijabi ya ba wa mutane da yawa mamaki
  • Yayin da suke yaba mata game da kwarewarta a iya wasan kwallon kafa, wasu mutane sun yi sha'awar sanin yadda ta koyi wasan sosai har haka

A kwanan nan ne aka dauki bidiyon wata budurwa ‘yar Najeriya, inda ta yadu a shafin Instagram tana buga wasan kwallon kafa daidai iyawarta.

Bidiyon ya baiwa jama'a mamaki a shafukan sada zumunta inda suka yi ta cancara mata yabo kan bajintar iya kwallon kafa.

Budurwa ta ba da mamaki yayin da take buga kwallon kafa
Gwana ta gwanaye: Musulma mai hijabi ta girgiza intanet yayin da ta nuna kwarewa a buga kwallo | Hoto: @hijabballer
Asali: Instagram

A cikin faifan bidiyon da ta wallafa ta shafinta na Instagram mai suna @hijabballer, an gan ta tana sanye hijabi kuma tana tsalle-tsalle a lokacin da take nuna kwarewarta.

Kara karanta wannan

"Aljanna Zai Muku Wahalar Shiga": Mutane Sunyi Martani Kan Wani Wasa Da MC Tagwaye Da Danuwansa Suka Yi Wa Jinjirarsa

Kalli bidiyon:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin 'yan Instagram

Bidiyon ya jawo cece-kuce daga mutane musamman masoya kwallon kafa wadanda suka bayyana sha'awarsu ta koyon fasahar taka leda kamar ta ta.

Adams Collins ya ce:

"Gaskiya kin fa kware. Kalli yadda kike aika kwallon nan sai kace wani wake."

Princess Jackrese ta ce:

"Ke kwararriyar 'yar wasa ce. Ta yaya kika koyi yin wasa da kwallon kafa haka? Wannan a zahiri abin mamaki ne."

Jennifer Okolo ta ce:

"Lallai, abin da ya burge ni shine yadda kike takalar ta ba tare da wata damuwa ba, da alama kin samu kwarewa daga ciki ne saboda wannan abu ya yi kyau."

Oma Odigie ya ce:

"Ina jin dadin ganin mutanen da suke buga kwallon kafa amma ni ban san yadda zan yi na buga ba, abin na sa ni nishadi sosai."

Kara karanta wannan

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

Soma Olivia ta ce:

"Kin kware sosai a kwallon kafa. Ya kamata ki fara tunanin tafiya mataki mafi girma."

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

A wani labarin, jarumar fina-finan Najeriya da suka shahara da Nollywood, Mercy Aigbe ta bayyana cewa za ta iya zama Musulma, kuma hakan ba komai bane.

Aigbe ta fadi haka ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da take bayyana yadda take jin dadin sabon salon shigar ta.

Jarumar dai ita ce mata ta biyu ga wani dan kasuwar harkar fina-finai, Kazim Adeoti wanda aka fi sani da Adekaz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.