A Shirye Muke Mu Janye Yajin Aiki, In Ji 'Kungiyar ASUU

A Shirye Muke Mu Janye Yajin Aiki, In Ji 'Kungiyar ASUU

  • Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ta ce ta gama duk wani tattaunawa da za ta yi da gwamnatin tarayya
  • Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban ASUU na kasa ya ce ko a yau gwamnati ta fada musu ta amince da UTAS za su janye yajin aiki gobe
  • Osodeke ya kuma ce gwamnati ta ki biyan malaman da ke yajin aikin albashinsu na watanni biyar da suka wuce

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ta ce a shirye ta ke ta janye yajin aikin game gari da ta ke yi a kasar, rahoton Daily Trust.

ASUU ta fara yajin aikin gargadin ne domin janyo hankali kan bukatunta, tun a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Shugabannin ASUU.
A Shirye Muke Mu Janye Yajin Aiki, Kungiyar ASUU. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

Daga bisani kungiyar ta ayyana cikakken yajin aiki, tana zargin Gwamnatin Tarayya da rashin gaskiya.

Da zarar gwamnati ta amince da UTAS za mu janye yajin aiki - Farfesa Osodeke

A hirar da aka yi da shi a Channels TV, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce kungiyar na jiran amsa mai kyau daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce:

"A bangaren ASUU, ana iya janye yajin aikin gobe, mun kammala tattaunawa, idan gwamnati ta kira mu daren yau cewa mu zo mu rattaba hannu kan yarjejeniya, za mu tafi.
"Gwamnati ta fada mana ta gama gwajin UTAS, mun amince da shi. Zuwa gobe, za mu iya janye yajin aiki. Mun gama (tattaunawa).
"Muna jira ne, kuma muna kallubalantar gwamnati. Yaushe za su saka hannu, kuma yaushe za su amince da UTAS? Wannan sune tambayoyi biyu da ya kamata mu tambayi gwamnati."

Osodeke ya ce gwamnati ta ki biyan malaman da ke yajin aikin albashinsu na watanni biyar da suka shude.

Kara karanta wannan

Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin gano yawan 'Yan Najeriya

ASUU ta dade tana kai ruwa rana da gwamnatin tarayya, kan abin da ta kira rashin cika yarjejeniya da suka yi a shekarar 2009.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164