Femi Otedola: Allah Ya Biya Wa Tinubu Bukatarsa Ya Zama Shugaban Kasar Najeriya

Femi Otedola: Allah Ya Biya Wa Tinubu Bukatarsa Ya Zama Shugaban Kasar Najeriya

  • Attajirin dan kasuwan Najeriya, Mr Femi Otedola ya yi wa dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023, Bola Tinubu addu'a
  • Otedola ya yi addu'ar Allah ya cika wa Tinubu burinsa na son zama shugaban Najeriya a zaben 2023 bayan karewar wa'adin Shugaba Buhari
  • Biloniyan Attajirin Otedola ya yi wa Tinubu wannan addu'ar ne bayan ya kai masa ziyara a birnin Paris da ke kasar Faransa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Biloniyan dan kasuwan Najeriya, Femi Otedola, ya yi wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bisa burinsa na zama shugaban kasa a 2023.

Otedola, a wani rubutu da ya wallafa a Twitter, ya bayyana murna bayan ziyarar da ya kai wa Tinubu a Paris, Faransa.

Femi Otedola da Bola Tinubu.
Femi Otedola: Allah Ya Biya Wa Tinubu Bukatarsa Ya Zama Shugaban Kasa. Hoto: @realfemiotedola.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Mai dakina ta na ajiye Bible dinta a gefen Qur’ani na, kuma a kwana lafiya inji Tinubu

Attajirin mai taimakon mutane, wanda ya bayyana Tinubu a matsayin 'babban abokinsa' ya yi addu'ar Allah ya cika wa Tinubu burinsa na zama shugaban kasa na gaba.

A shafinsa na Twitter, ya rubuta:

"A kowanne lokaci ina cike da murna yayin ziyartar Babban Aboki Na Asiwaju Ahmed Bola Ahmed Tinubu @officialBAT.
"Allah ya biya masa burinsa na zama Shugaban wannan gagarumar kasar Najeriya ...F.Ote$."

Wani Tsohon Bidiyon Biloniya Femi Otedola Cikin Motar Haya Ba Tare Da Fasinjoji Sun Gane Shi Ba Bayyana

A wani rahoton, wani tsohon bidiyon attajirin dan kasuwa Femi Otedola ya sake bulla a shafukan intanet, abin da ya farantawa mutane da dama rai.

Bisa dukkan alamu, wasu shekaru da suka gabata, fittacen dan kasuwan ya shiga motar haya 'molue' ba tare da fasinjojin da ke motar sun gane ko shi wanene ba.

Bidiyon ya nuna Otedola yana zaune kusa da wata mata wacce ke tallar kayayakinta ga mutanen da ke cikin motar hayan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel