Adadin wadanda aka kashe a Shiroro ya kai 48, ciki akwai Soji 34: Inji shugaban matasan yankin

Adadin wadanda aka kashe a Shiroro ya kai 48, ciki akwai Soji 34: Inji shugaban matasan yankin

  • Shugaban matasan yankin Shiroro ya ce sun kara gano wasu gawarwakin jami'an tsaron da aka kashe a satin da ya gabata
  • Adadin mutanen da aka kashe ya tashi daga 42 zuwa 48 wanda ya kunshi sojoji 34, ‘yan sandan mobile guda 8
  • A satin da ya gabata wasu yan bindiga suka yi wa sojoji kantar bauna lokacin da suka je kai dauki wani hari da aka kai wurin hakar ma’adinai a shiroro

Jihar Neja - Rahotanni da ke fitowa na nuna cewa an gano karin gawarwakin sojoji da jami’an ‘yan sanda da aka kashe a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai garin Shiroro na jihar Neja rahoton jaridar VANGUARD.

Kara karanta wannan

Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a wata jiha

Sani Kokki, shugaban matasan na jihar Neja, ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace adadin wadanda suka mutu ya kai 48.

Shugaban matasan, wanda ya zanta da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja, ya bayyana cewa bayan gawawarki 42 da aka gani a farko, an sake gano wasu gawarwaki a ranar Asabar, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 48.

LOLO N
Adadin wadanda suka mutu a Shiroro ya kai 48 inji shugaban matasan yankin :FOTO LEADERSHIP
Asali: Twitter

Adadin mutane da suka mutu sun hada da sojoji 34, ‘yan sandan mobile guda takwas da kuma mazauna yankin shida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu ‘yan bindiga ne suka yi wa sojojin kwanton bauna a lokacin da suke amsa kiran da aka yi musu na wani hari da aka kai a wurin hakar ma’adinai a yankin.

Bayan kashe jami’an da suka je kai dauki, maharan sun yi awon gaba da wasu daga cikin masu hakar ma’adinai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Aikin Hajji :Jami’in NAHCON ya karkatar da kudin maniyyata a Neja

Jihar Neja : Maniyyatan daga karamar hukumar Bida ta jihar Neja ba za su yi aikin Hajjin bana ba saboda jami’in Alhazai na yankin (APO), Nma Ndagana, ya kasa bayyana miliyoyin kudi da aka biya a asusunsa bankin sa.

Jaridar Daliy Trust ta tattaro cewa kimanin mahajjata 150 ne suka biya kudi a asusun bankin APO kamar yadda ya umarce su a maimakon su biya a asusun da hukuma ta kebe na bankin Jaiz

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa