Labari mai dadi: ASUU ta kafawa FG sharudda 2 tak, tace ana cikasu gobe za a koma karatu

Labari mai dadi: ASUU ta kafawa FG sharudda 2 tak, tace ana cikasu gobe za a koma karatu

  • Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta karba tsarin biyan albashi na UTAS
  • Kamar yadda Farfesa Rmmanuel Osodeke, shugaban ASUU ya bayyana, yace matukar aka aminta da UTAS kuma aka sanya hannu kan yarjejeniyar 2009, zasu janye yajin aiki
  • Farfesan ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya tana cika sharuddan nan biyu, ko gobe ne zasu iya komaawa bakin aikinsu

Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i, ASUU, ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta karba tsarin biyan albashi na University Transparency and Accountability, UTAS, domin ta janye yajin aikin da ta tsunduma.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya sanar da hakan yayin zantawa da gidan talabijin na Channels a daren Litinin, yace zasu cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta karba UTAS kuma ta karrama yarjejeniyar su ta 2009.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

ASUU da gwamnatin tarayya
Labari mai dadi: ASUU ta kafawa FG sharudda 2 tak, tace ana cikasu gobe za a koma karatu. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Idan za a tuna, ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 wanda a ranar Litinin din nan ne ta cika kwanaki 140.

ASUU da gwamnatin tarayya sun gaza daidaitawa inda suka kafa hujja da kin cika yarjejeniyar 2009 da gwamnatin tarayya ta yi da kungiyar, jaridar Leadership ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bukatun dake cikin yarjejeniyar sun hada da cewa za a dinga jin halin da aikin Malaman jami'o'in ke ciki duk shekara biyar, matsalar albashi da alawus, gyaran jami'o'in da sauransu. A yanzu akwai matsalar UTAS da kuma rashin daidaito na IPPIS.

Osodeke yace, "Gwamnati ta sanar da mu cewa ta gama gwada UTAS kuma ta saka hannu a kan yarjejeniyar, mu kuma gobe zamu janye yajin aiki.
"Mun kalubalanci gwamnatin tarayya, yaushe zasu sa hannu kan yarjejeniyar? Yaushe zasu amince da UTAS? Wadannan sune tambayoyi biyu muhimmai da muke yi wa gwamnatin," yace.

Kara karanta wannan

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis

A wani labari na daban, Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'in, ASUU, tace gwamnatin tarayya bata gayyaceta wani taro ba a ranar Alhamis.

A ranar Laraba da ta gabata, Chris Ngige, ministan kwadago da aikin yi, yace gwamnatin tarayya nan babu dadewa za ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta tsunduma watanni hudu da suka gabata.

Ya kara da cewa, matsalolin bangaren biyan albashi da salon da gwamnatin tarayya ta zo da shi wanda kungiyar bata aminta da shi ba duk za a shawo kan shi a taron da za ta yi da kungiyar a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng