Hajjin Bana: Har yanzu maniyyatan Najeriya 8,000 suna gida
- Maniyyatan Najeriya da dama basu san makomar su ba yayin da wa'adin dibar su zuwa kasar mai tsarki ya kusan kurewa
- Gwamnatin Kasar Saudiyya ta karawa Najeriya sa'o'i 48 dan kammala kwashe duka alhalzanta zuwa kasar
- Shugaban kungiyar masu aikin Hajji da Umrah ta Najeriya ya ce maniyyata da dama baza su samu tafiya ba
Najeriya : Duk da Karin wa’adin diban maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki da gwamnatin Saudiyya tayi, har yanzu akwai rashin tabbas akan makomar maniyyata da dama kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Sa’o’i 24 ya rage wa’adin da Saudiya ta karawa Najeriya ya cika amma Sama da maniyyata 8,000 ba su san makomar su ba, yayin da suke jiran jirgin da zai kwashe su zuwa kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da labarin farin ciki a ranar Litinin da ta gabata cewa Saudiyya ta kara wa Najeriya wa’adin sa’o’i 48 domin kwashe dukkan maniyyatan da suka rage zuwa aikin Hajji.
Maimakon a rufe kwashe maniyyata ranar Litinin Karin wa'adin ya maida kusan zuwa ranar Laraba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da labarin Karin wa’adi ya kwantar da hanklin maniyyatan da suka makale a fadin kasar, har yanzu akwai fargaba ganin yadda lokacin wa’adin da aka kara ya kusan kurewa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa, zuwa safiyar Litinin din nan an kwashe maniyyata 27,359 daga cikin 33,971 yayin da kimanin maniyyata 5,641 suna jira a kwashe su.
Shugaban kungiyar masu aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) na kasa, Alhaji Nasidi Yahaya ya ce,
“Ba mu gama warware matsaloli da dama da ya shafi tafiyar mahajjata ba. Tabbas da yawa daga cikin mahajjata baza su samu tafiya ba, duk da shirya jiragen ceto da muka yi. Muna jira mu ga yadda abubuwa za su kasance".
Babu yankin da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai, inji kungiyar Afenifere
A wani labari kuma, Kungiyar Afenifere ta bukaci ‘yan siyasa daga yankin Kudu maso Yamma da su hada kai da sauran shiyyoyi biyar na kasar domin tabbatar da aniyar tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, na zama shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa ya yiwu. rahoton PUNCH
Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Michael Ogungbemi, ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kungiyar gwamnonin APC, yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka janye wa Tinubu da ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi ruwa da tsaki dan ganin ya samu damar tsayawa takarar.
Asali: Legit.ng