Duk da ana zarginsa da wawure biliyoyi, tsohon gwamna ya raba shanu 370, raguna 3,500 na sallah

Duk da ana zarginsa da wawure biliyoyi, tsohon gwamna ya raba shanu 370, raguna 3,500 na sallah

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulazizi Yari, ya raba shanu 370 da raguna 3,593 ga jama'ar jihar ana dab da shagalin babbar sallah
  • Kamar yadda jagoran rabon, tsohon shygaban APC na Zamfara, Lawal Liman ya sanar, an raba su ne ga marasa karfi, shugabannin APC da kungiyoyi
  • Duk da ana zargin Yari da satar biliyoyin kasar nan, ya raba ragunan har ga malaman addini tare da kungiyoyin mata

Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda ake zargi da satar biliyoyin kudin kasa, ya siya shanu 370 wadanda ya raba wa shugabannin APC da marasa karfi da wasu kungiyoyi don shagalin babbar sallah a 2022.

Shugaban kwamitin rabawa kuma tsohon shugaban APC na jiha, Lawal Liman, ya bayyana hakan yayin rarraba shanun ga jama'a a Gusau ranar Asabar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shawarci Obi da ya zama abokin takararsa, ya bayyana muhimman dalilai

Abdulaziz Yari
Duk da ana zarginsa da wawure biliyoyi, tsohon gwamna ya raba shanu 370, raguna 3,500 na sallah. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: Facebook

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito yadda gwamnan a farkon makon nan ya rarraba raguna 3,593 ga jama'a a jihar domin shagalin sallah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Liman yace wannan kyautar an yi ta ne domin taimakawa marasa karfi wurin shagalin babbar sallah cikin sauki.

Yace wadanda suka amfana sun hada da tsoffi da sabbin shugabannin APC daga gunduma 147 da kananan hukumomi na jam'iyyar.

"Sauran wadanda suka amfana sun hada da malamai, matasan APC da kungiyoyin mata, kungiyoyi masu zaman kansu tare da shugabannin al'umma a jihar," Liman yace.

Ya yaba wa tsohon gwamnan kan yadda ya taimakawa jama'ar jihar ballantana jama'ar yankinsa.

Liman yayi kira da Musulmai da su yi amfani da lokacin idin babbar sallah wurin addu'ar zaman lafiya da daidaito a jihar da kasar baki daya.

EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Legit.ng ta ruwaito muku cewa, Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta damke tsohon gwamna Abdulaziz Yari kan binciken da hukumar ke yi game da kudaden da ake zargin akanta janar Ahmed Idris da kwashewa.

Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, an kama shi ne a yammacin Lahadi a gidansa da ke Abuja, kwanaki kadan bayan da yayi nasarar samun tikitin takarar kujerar sanata na Zamfara ta yamma wanda za a yi a shekara ta gaba. Ya yi nasara babu abokin hamayya, Premium Times ta ruwaito.

Ana zargin dakataccen AGF Idris da handamar wasu kudade, lamarin da yasa EFCC ta damke shi tun ranar 16 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng