Borno: Yadda N414m tayi batan-dabo daga asusun jiha a karkashin mulkin Zulum

Borno: Yadda N414m tayi batan-dabo daga asusun jiha a karkashin mulkin Zulum

  • Rahoton odita janar na jihar Borno ya bayyana yadda wasu N414 miliyan suka yi batan dabo a 2020 karkashin mulkin Gwamna Zulum
  • Kamar yadda Shettima Bukar ya bayyana, ma'aikatun da rashawar ta shafa sun hada da na gidaje da wutar lantarki, noma da wasu ma'aikatu 7
  • Ya bayyana yadda dukkan ma'aikatun suka yi biris da takardun tuhumar da aka aike musu ba tare da wani bayani kan kudaden ba

Borno - Gwamnan jihar Borno, Babgana Zulum, ya yi fice kan yadda yake daukar matakan yaki da rashawa a jiharsa. Amma rahoton odita janar na jihar na 2020 ya ci karo da abinda gwamnan ya tsayu a kai.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ma'aikatu biyar na jihar sun kasa bayyana inda suka yi da N414 miliyan daga asusun jihar.

Kara karanta wannan

2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Tinubu Zai Zabi Mataimakinsa Daga Cikinsu

Gwamna Zulum na jihar Borno
Borno: Yadda N414m tayi batan-dabo daga asusun jiha a karkashin mulkin Zulum. Hoto daga @GovBorno
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Odita janar na jihar, Shettima Bukar, yace an mika takardun tuhuma 29 ga ma'aikatun saboda rashin takardun da ke nuna yadda suka kashe kudaden a shekarar. Da yawa daga cikin tuhumar ba a amsa su ba.

Tara daga cikin tuhume-tuhumen an mika su ne ga ma'aikatu biyu - ma'aikatar lamuran cikin gida, yada labarai da al'ada da kuma ma'aikatar gidaje da wutar lantarki, wadanda suka kashe N22,155,800 ba tare da rasit ko wata shaida ba kuma babu haitimin odita jana na jihar kafin fitarda kudin.

“Hakazalika, a yayin rubuta rahoton shekarar 2019, akwai wasu tuhuma wadanda ba a saka ba a rahoton, wanda kuma dole a saka su a rahoton odita janar na 2020.
"Akwai tuhume-tuhume 20 da jimilla kudadensu suka kai N392,450,423.29 wadanda aka mika ga ma'aiktau hudu. Su ma ba a yi martani a kansu ba har a yayin rubuta wannan rahoton," Shettima yace.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

Ma'aikatu hudun da ake tuhuma a 2019 sune na noma da kiwo, gidaje da wutar lantarki, ma'aikatar addinai da ilimi na musamman da kuma ma'aikatar kananan hukumomi da lamuran masarautu. Sun kasa bayyana yadda suka yi da N414,606,223.29.

Odita janar din ya alakanta wadannan matsalolin da rashin tsarin kula da ma'aikatun wanda ya bar da yawa daga cikin shaidun fitar kudi babu takardun da suka dace domin goyon bayan dalilin fitar da su.

Rahoton ya kara da bayyana wasu cikas da ake samu wurin kawo takardu masu muhimmanci da suka shafi kudi da kasafi, Premium Times ta ruwaito.

Hotunan Zulum a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, ya bai wa masu komawa gida N.5b

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da rabin biliyan daya, Daily Trust ta ruwaito. ‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng