Tashin Hankali: An Ceto Yara 50 A 'Kurkukun' Karkashin Kasa A Wani Cocin Jihar Ondo
- Jami'an yan sanda a Jihar Ondo sun ceto wasu yara da mutane a kalla 50 a wani gida da ke karkashin coci a Valetino
- An kama faston cocin da wasu mutane da ke hada baki da shi an kuma tafi da su hedkwatar yan sanda na Jihar Ondo
- Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Ondo Funmi Odunlami ta tabbatar da kamen da yan sandan suka yi
Jihar Ondo - A kalla yara guda 50 ne aka ceto a wani gidan karkashin kasa da ke kasan wani coci a wani gari, Jihar Ondo.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an sace yaran ne aka kuma ajiye su a wani gidan karkashin kasa a cocin.
An kama faston cocin da wasu da ke aiki tare da shi yayin da yan sanda suka kai samame wurin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bidiyon yaran da aka sace ya karade shafukan sada zumunta.
An hange su a motan sintiri na yan sanda wacce ta kai su caji ofishin yan sanda.
A wata murya a bidiyon na cewa, "Yara ne da aka sace aka kuma gano su a wani kurkukun karkashin kasa da ke cocin Valentina na Ondo.
"An kama faston cocin da wasu mambobi kuma suma an gan su a cikin motar sintirin na yan sanda."
Martanin yan sanda kan gano yaran
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, Funmi Odunlami, ta tabbatar da gano yaran da yan sandan suka yi.
Odunlam ya ce wadanda aka ceto din an kai su hedkwatar rundunar yan sanda da ke Akure.
A cewar ta, "ban da cikakken bayani a yanzu amma ana kawo wadanda aka ceto zuwa hedkwata.
"Zan baka karin bayani da zarar na samu daga wurin DPO."
Fasto Ya Faɗa Wa Mabiyansa Tashin Duniya Ya Zo, Ya Ce Kowa Ya Biya N310,000 Don a Buɗe Masa Kofar Zuwa Aljanna
A wani rahoton, yan sanda a Jihar Ekiti sun gayyaci wani fasto da ake zargin cewa ya yi wa mabiyansa wa'azin cewa karshen duniya ta zo kuma su tara masa kudade don ya bude musu kofar zuwa aljanna, rahoton Premium Times.
Yan sandan sun ce faston ya bukaci mambobinsa su koma wani sansani a Araromi-Ugbesi a Omuo-Oke-Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta Gabas na jihar 'domin su shirya wa karshen duniya.'
Asali: Legit.ng