Zaben fidda gwani : Shugaban Ohanaeze yayi fashi baki a karo na farko
- Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo yace manyan yan siyasa Najeriya sunyi nasarar dakile kabila Ibo daga fitar da dan takarar shugabankasa
- Ambasada Farfesa George Obiozor ya ce duka manyan jam'iyyun kasar sun ki ba dan kabilar Ibo daman tsyawar takarar shugaban kasa
- Obiozor ya zargi Atiku da Tinubu da kashe makudan daloli wajen siyan kujerar shugaban kasar Najeriya
Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Ambasada Farfesa George Obiozor, ya mayar da martani kan zaben fidda gwani na shugaban kasa da jam'iyyar All Peoples Congress da babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, suka gudanar dan takarar zaben 2023.
Duka yan siyasan shiyar kudu maso gabas da suka tsaya takarar fidda da gwani a manyan jami’yyun guda biyu sun fadi warwas, inda wasu basu samu kur’ia ko daya ba a zaben, duk da ganin cewa yankin ya kamata mulki ya dawo hanun su bisa adalci da rikon amana na kudirin mulkin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa, rahoton PUNCH
Yayin da Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas daga yankin Kudu maso Yamma, ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daga yankin Arewa maso Gabas ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Amma Obiozor yayi tsokaci na farko a safiyar Asabar a wata sanarwa mai taken: "Menene Najeriya ke so daga yan kabilar Ibo?"
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace, “
Yanzu ta tabbata cewa jiga-jigan siyasar Najeriya sun yi nasarar dakile yankin Kudu maso Gabas damar fitar da shugaban Najeriya a 2023 ".
Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya
A wani labari, Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha ya jaddada kudirinsa na zama shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar Action Alliance, AA, a zaben 2023 ya ce a shirye ya ke "ya sadaukar da rayuwarsa don Najeriya da walwalar yan Najeriya".
Al-Mustapha ya ce fatansa shine ya zama shugaban Najeriya kuma ayyukan da ya yi a baya sun isa zama hujja a kansa.
Asali: Legit.ng