Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa dan majalisar wakilan jihar Edo mai ci rasuwa
- Dan majalisar dokokin jihar Edo, Hon. Jude Ise-Idehen ya riga mu gidan gaskiya bayan 'yar karamar rashin lafiya
- Rahoton da muka samu ya bayyana cewa, dan majalisar ya rasu a yau Juma'a, duk da cewa ba a bayyana hakan a hukumance ba
- Hon. Jude Ise-Idehen ya lashe tikitin komawa majalisar dokokin jihar a zaben fidda gwanin da aka kammala kwanan nan
Edo - an majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Egor/Ikpoba-Okha na jihar Edo, Hon. Jude Ise-Idehen ya mutu, The Nation ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar ya rasu ne da safiyar Juma’a sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ko mecece ba.
Kakakin majalisar, dan majalisa Benjamin Kalu ya tabbatar da mutuwar abkin aikin nasa amma ya ce har yanzu majalisar ba ta san halin da ake ciki ba.
Kalu ya ce har yanzu yana kan magana da Shugabancin Majalisar kuma yana iya fitar da sanarwa a hukumance daga baya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ise-Idehen, mai shekaru 52 kuma dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya lashe tikitin jam’iyyarsa na neman sake tsayawa takara a babban zaben 2023 mai zuwa, inji rahoton Punch.
Ta tabbata: INEC ta amince da takarar gwamnan Kano ga dan janar Abacha a PDP
A wani labarin, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta sa idon basira a zaben fidda gwani da ya samar da Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Kafin bayanin na INEC dai an yi ta cece-kuce kan wanda hukumar za ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamna tsakanin Mohammed Abacha da Sadiq Wali.
Kwamishinan zabe na yanki (REC), Farfesa Riskuwa Shehu, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Kano, a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, in ji jaridar The Guardian.
Asali: Legit.ng