Buhari ya jinjinawa sojojin da aka kashe a jihar Neja a ranar Alhamis

Buhari ya jinjinawa sojojin da aka kashe a jihar Neja a ranar Alhamis

  • Yan ta'adda sun kai wa kamfanin hakar gwal farmaki a jihar Neja
  • Jami'an tsaro da dama sun rasa rayukan su a harin yan bindiga a jihar Neja
  • Buhari ya Bukaci yan Najeriya su yi wa wadanda akayi garkuwa da su adu'a su dawo cikin koshin laifya

Jihar Neja : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana harin da aka kai ranar Alhamis a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja a matsayin hari kai tsaye ga zaman lafiyar Najeriya.

Shugaban kasar a wata sanarwa da mai magana da yawun bakin sa Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a, ya ce maharan ba za su tafi ba tare da an hukunta su ba kamar yadda jaridar Dailytrust ta rahoto.

Ya ce lamarin ba zai shafi yaki da ake yi da ta'addanci da gwamnatin sa ke yi ba, domin kasar ta hada kai wajen kawar da wadannan "shaidanun" da "'yan ta'adda" wadanda ya kuma bayyana su a matsayin "kaska".

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

sojoj
Buhari ya jinjinawa sojojin da aka kashe a jihar Neja a ranar Alhamis
Asali: Facebook

Buhari ya jinjinawa jami’an tsaron da suka rasa rayuwakan a lokacin da yan ta’adan suka kaimu su hari. Kuma yayi kira ga yan Najeriya da su yiwa mutanen da akayi garkuwa da su adu’a dawo su cikin koshin lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce “Muna jinjinawa jami’an tsaron mu, musamman gwarazan da suka ba da rayukan su wajen yaki da ta’adanci. Suna cikin mutane mafi daraja da suka fito daga kasar nan, kuma baza mu manta da kowanne daga cikim su ba.

“Abin bakin ciki ne ganin yadda har yanzu Najeriya na fama da matsalar ta’aadanci. Amma baza muyi kasa a gwiwa ba har sai mun ga karshen su.

Yan ta’ddan sun kashe sojoji 15 da yansanda 7 a lokacin da suka musu kantar bauna a kamfanin hakar gwal dake kan kulawar yan kasar Chana a Ajata-Aboki Gurmana a karamar hukumar Shiroro.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

Shiroro yana dauke da tashar samar da wutar lantarki , wanda ya kunshi ruwa kogin Kaduna da ya wuce ta jihar Neja, tashar shiroro yana samar da wuatar lantarki mai karfin megawatts 600 (Hp 800,000), wanda ya isa ya kai wa gidaje 404,000 wuatar lantarki.

A wani labari kuma yan bindigan sun sako ma'aikatan lafiyan da suka yi garkuwa da su a yankin Ɗansadun, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa