Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗinsu a Enugu

Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗinsu a Enugu

  • Ɗalibai mata sun sha da ƙyar yayin da wata Gobara ta tashi a gidan kwanan su na kwalejin Ilimi ta Peaceland, jihar Enugu
  • Rahoto ya nuna cewa wutar ta fara ne daga ɗaki guda, kuma ta aikata babbar ɓarna da ya haɗa takardun karatun Diplomar ɗalibai
  • Wata ɗaliba ta bayyana cewa suna zargin wani ne ya kunna wutar Lantarki kuma ya mance bai kashe ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Enugu - Ɗaruruwar ɗalibai a kwalejin ilimi da ke Peaceland, jihar Enugu sun tsallake rijiya da baya ta ƙananan hanyoyi yayin da wuta ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai mata.

Makarantar ta yi hannun riga da wani sashin jami'ar kimiyya da fasaha ta Enugu, kusa da shahararren Junction ɗin Nkpokiti a yankin Independence Layout, jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Wata matar aure ta sa yan bindiga sun yi garkuwa da Mijinta kan wani saɓani tsakanin su

Jaridar Punch ta rahoto cewa da yawan ɗaliban sun jikkata yayin da suke rige-rigen fita daga wurin sabida tashin hankalin da suka shiga a harabar Hostel ɗin.

An samu Gobara a PCEE
Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗinsu a Enugu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Bayanai sun ci karo na juna kan musabbabin da ya haddasa gobarar yayin da wasu ke cewa hanyoyin wutar Lantarki ne suka haɗu, wasu na ganin ɗalibai ne suka bar abun da ake jona wa wuta a kunne suka tafi aji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da babu wanda ya rasa rayuwarsa a gobarar, wasu bayanai daga ma'aikatan makarantar sun ce wutar ta laƙume rufi, cilin, tagogi, gadajen kwanciya da sauran kayayyaki da suka kai na miliyan N30m.

Haka zalika mummunar gobarar ta cinye wasu daga cikin takardu masu muhimmanci mallakin ɗalibai.

Yadda gobarar ta illata ɗalibai

Wasu lakcarorin kwalejin da suka nemi a sakaya bayanan su, sun ce ba dan ɗaukin hukumar kwana-kwana kan lokaci ba da wutar da ƙone baki ɗaya Hostel ɗin.

Kara karanta wannan

Hajji 2022: Wani Alhaji ɗan Najeriya ya maida makudan kuɗin da ya tsinta a jaka a Madinah

Wani Malami ya ce wutar ta fara daga ɗaki ɗaya dake sama, kuma ta kone takardun shaidar kammala Diploma ND da sauran takardun ɗalibai.

Wata ɗaliba da ta bayyana sunanta da Chinwe Odo, ta ce:

"Muna azuzuwa lokacin da muka ji ƙarar fashewar wani abu, da muka fito sai muka hangi wuta na ci rigi-rigi a ɗaya daga cikin ɗakunan Hostel."
"Wasu daga cikin mu, musamma ɗalibai da ke karatun babban Diploma (HND) sun zo da takardun shaidar karamar Diploma (OND) saboda an faɗa mana za'a zo tantance mu daga Abuja. Duk takardun sun ƙone."
"Duk da ba kowa a ɗakin da wutar ta fara amma muna zargin wani ne ya kunna abun wuta ya mance bai kashe ba. Sakamakon haka mun yi asara da yawa. Rufin wurin, Cilin da sauran abubuwa."

Har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan rahoton, hukumar kwalejin ba ta fitar da sanarwa a hukumance game da gobarar ba.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

A wani labarin na daban kuma Babban Ɗan Farfesa Ango Abdullahi Ya Rigamu Gidan Gaskiya a Abuja

Shugaban ƙungiyar Dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya yi rashin babban ɗansa, Isa Ango Abdullahi jiya Alhamis da yammaci.

Bayanai daga Zariya sun tabbatar da cewa za'a dawo da gawarsa daga birnin tarayya Abuja yau Jumu'a domin yi masa Jana'iza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262