Jirgin Kasan Abj-Kd: Iyalan Fasinjoji Sun Koka Kan Labarin Harbin 1 Daga Cikin Wadanda aka Sace

Jirgin Kasan Abj-Kd: Iyalan Fasinjoji Sun Koka Kan Labarin Harbin 1 Daga Cikin Wadanda aka Sace

  • Iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun kai kukansu majalisar tarayya kan yadda rayuwar 'yan uwansu ke cikin hadari
  • Hakan yazo ne bayan samun rahoton yadda masu gadin fasinjojin suka bindige daya daga cikinsu tare da ji masa matsanantan raunuka
  • Sai dai, 'yan majalisar sun yi alkawarin yin duk abun da ya dace karkashin ikonsu don ceto rayuwar salahan bayin cikin kankanin lokaci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Iyalan fasinjojin da aka yi garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun bukaci gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen ganin an saki wadanda aka yi garkuwa dasu bayan samun rahoto yadda aka bindige daya daga cikinsu.

Iyalan sun ziyarci wasu 'yan majalisar tarayya a ranar Laraba, inda suka bukaci gwamnati da ta taimaka wajen nemo wadanda aka sacen.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun harba 1 daga cikin fasinjojin jirgin Abj-Kd dake wurinsu

Bamidele Salam 'dan jam'iyyar PDP na jihar Osun, Mansur Sora, APC daga Bauchi da sauran guda 10 a makon da ya gabata sun kawo batun a majalisar, inda suka yi kira ga sakin wadanda aka yi garkuwa dasu.

Messrs Salam da Soro ne suka tarbi iyalan a gidan gwamnatin tarayya a Abuja.

Yayin magana a madadin iyalan, matar wani wanda aka yi garkuwa da shi, Matilda Kabir, ta ce rashin tabbacin shi ne kisa. A cewarta ba su san waye wanda cikin wadanda aka yi garkuwa dasu za a sake hara ba.

Matar Kabir ta ce tsawon kwanaki 94, iyalan sun kasance cikin dari-dari ba tare da sanin makomar masoyansu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Labarin da muka samu a safiyar yau shi ne yadda aka bindige daya daga cikinsu. Mijina yana wurin. Bamu san wa za a sake hara ba. 'Yan Najeriya su taimaka. Mijina yana can tsare," tace.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

Aminu Usman, wanda aka yi garkuwa da 'dan uwansa ya bukaci 'yan majalisa da su taimaka wajen hurawa gwamnati wuta wajen ceto wadanda aka yi garkuwa dasu.

Yayin martani, Mr Bamidele ya ce majalisar na shirya hukumomin da suka dace kan lamarin.

Ya tabbatarwa iyalan cewa gwamanati za ta yi iya kokarinta don ceto rayukan wadanda aka yi garkuwa dasu.

"Yayin da muke magana da gwamnati, muna cigaba da magana da masu sasanci - wadanda ke magana da masu garkuwa da mutane sannan muna sa rai da izinin Ubangiji za mu iya tabuka wani abu cikin kankanin lokaci," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng