Yanzun nan: An ga watan babbar sallah a Najeriya, sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa
- Sarkin Musulmi ya ayyana ranar 30 ga watan Yuni a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, watan babbar sallah
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da musulman Najeriya ke ci gaba da jiran sanarwar sarkin gabanin babbar sallah
- Musulmin Najeriya za su yi sallah babba a ranar 9 ga watan Yulin 2023, daya daga cikin bukuwa masu daraja
Sokoto - Sarkin Musulmi na Najeriya, Alhaji Sa'adu Abubakar ya ayyana gobe Alhamis 30 ga watan Yuni a matsayin daya ga watan Dhul Hijjah.
A ranar goma ga kowane watan Dhul Hijjah ne musulman duniya ke murnar babbar sallah, bikin shekara-shekara mai daraja a idon duniya.
A sanarwar da kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmin ta fitar a Twitter, an bayyana bayanan sarkin, inda aka ce daga baya zai fadi hakan a hukumance.
Sanarwar ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Assalaamu alaikum, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni a matsayin ranar daya ga watan Dhul Hijjah.
"Majalisar Sarkin Musulmi za ta fitar da wata sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba."
An ga jinjirin watan Babbar Sallah a Saudiyya
A wani labarin, hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul-Hijjah, watan babban Sallah yau Laraba 29 ga watan Dhul-Qa'adah 1443. Hakan na nufin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, zai zama ɗaya ga wata.
Ganin watan na nuni da cewa al'ummar Musulmi a Saudiyya zasu gudanar da babbar Sallah (Eid-El-Adha) ranar Asabar 9 ga watan Yuni, 2022dai-dai da 10ga watan Dhul-Hijjah 1443.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shafin da ke kula da manyan masallatai biyu masu tsarki Haramain Sharifai, ya fitar a Facebook.
Asali: Legit.ng