Rashin Tsaro: Buhari ya gaza bibiyar kalamansa da aiki, 'Dan majalisar wakilai na APC

Rashin Tsaro: Buhari ya gaza bibiyar kalamansa da aiki, 'Dan majalisar wakilai na APC

  • 'Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kachia da Kagarko, Gabriel Zock ya ce shugaba Buhari da APC sun gaza cika alkawarin shawo kan matsalar tsaro da suka yi yayin kamfen
  • Gabriel Zock, wanda 'dan jam'iyyar APC ne ya ce a matsayin shugaban kasa na kwamandan rundunar sojin kasa idan da suna so zakulo 'yan ta'addan zasu iya yin hakan
  • A cewarsa, idan har hukumomin tsaro zasu iya amfani da rahotanni da bayanan sirri, yayi imani da cewa matsalar ba zamta dauki tsawon watanni shida ba

Gabriel Zock, 'dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kachia da Kagarko a tarayya, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza tsayawa kan maganarsa da daukar mataki kan matsalar rashin tsaro a Kaduna.

'Dan majalisar jam'iyyar APC ya fadi hakan ne a shirin sunrise daily na Channels Television a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abinda Muka Tattauna da Obasanjo Yayin da ya Kawo Min Ziyara, Ango Abdullahi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Rashin Tsaro: Buhari ya gaza bibiyar kalamansa da aiki, 'Dan majalisar wakilai na APC. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A wata takarda da tazo bayan 'yan bindiga sun ja kunnen mutane Birnin-Gwari da kada su kuskura su shiga harkar siyasa, Zock ya cee shugaban kasa da jam'iyya mai mulki sun gaza cika alkawuran kawo karshen matsalar tsaro da suka dauka yayin kamfen.

"Ni 'dan APC ne; amma ba zan wuce wannan iyakar ba saboda hakan na da hatsari," a cewarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun yi kamfen a 2014 a kan tsaron kasa kuma yau muna da mafita ga wadannan lamurran tsaron amma ba a bamu damar kawo wadannan mafitar ba.
"Gwamnatin yanzu bata tabuka komai don kawo karshen matsalar tsaro. Zan iya ce muku basa kokarin.
"Shugaban kasa shi ne babban kwamandan sojin Najeriya. Ya kamata a bada umarni ga hukumomin tsaron ya kawo mafita bayan daukar shekaru bakwai.
"Gwamnati za ta iya zakulo ko waye kuma a kowanne lokaci idan suna so. Nayi imani da babu abun da suke yi don zakulo 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

"Dukkansu 'yan Najeriya ne kuma ba a kasashen ketare suke zaune ba. Idan har jami'an tsaro zasu iya amfani da rahotannin sirri da bayanai, nayi imani matsalar ba za ta kai watanni shida ba.
"Nayi imani shugaban kasa bai tsaya a kan kalamansa da matakai ba."

Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kaddamar da kwamitin tsaro guda 4 gami da samar da motoci 20 kirar Hilux da babura 1,500 don fara daukar matakai. Sakataran watsa labaran gwamnan, Jamilu Iliyasu Magaji ne ya bayyana hakan ranar Talata.

Kwamitin sune kwamiti na musamman don tattara bayanan sirrin ta'addanci, kwamitin kula da tsaron anguwa (CPG), kwamitin gurfanar da masu laifukan da suka shafi ta'addanci, da kwamitin tabbatar da tsaron jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng