Dhul-Hijjah: Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban jinjirin watan babbar Sallah

Dhul-Hijjah: Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban jinjirin watan babbar Sallah

  • Fadar mai martaba sarkin Musulmi da ke Sokoto ta umarci mutane su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah ranar Laraba
  • Sanarwan ta buƙaci ɗaukacin al'ummar Musulmin Najeriya su kai rahoto ga hakimi ko Dagaci da zaran sun ga watan
  • Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya roki Allah SWT ya cigaba da dafa wa musulmai wajen yin ibadar da aka ɗora musu

Sokoto - Sarkin Musulmai kuma shugaban majalisar Ƙoli ta shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah daga ranar Laraba.

Sultan Abubakar ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata ya fitar a shafinsa na Facebook ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin shawarwari kan harkokin Musulunci.

Kara karanta wannan

'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai

Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar na III.
Dhul-Hijjah: Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban jinjirin watan babbar Sallah Hoto: Daular usmaniyya/facebook
Asali: Facebook

Sanarwar ta tunatar da al'umma cewa ranar Laraba, 29 ga watan Dhil-Qa'adah, 1443 wacce ta zo dai-dai da 29 ga watan Yuni, 2022, ita ce ranar farko da ya kamata a duba wata.

Wani sashin sanarwan daga fadar sarkin Musulmin ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna sanar da Al'ummar Musulmi cewa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, wanda ya zo dai-dai da 29 ga watan Dhul-Qa'adah, ita ce rana ta farko da ya kamata a fara duban jinjirin watan Dhul-Hijjah 1443."
"Saboda haka ana buƙatar Musulmai su duba jinjirin watan ranar Laraba, kuma su kai rahoto da zaran sun gan shi ga hakimi ko Dagacin ƙauye mafi kusa da su don aika wa fadar Sultan."

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya roki Allah SWT ya cigaba da taimaka wa al'ummar Musulmai wajen sauke nauyin da Addini ya ɗora musu.

Muhimmancin Dhul-Hijjah a wurin Musulmai

Kara karanta wannan

Gwamnatin Yobe ta baiwa ma’aikata hutun kwanaki 3, ta bayyana dalili

Watan Dhul-Hijjah shi ne wata na 12 kuma wata na ƙarshe a jerin watannin Addinin Musulunci, kuma a cikinsa ne maniyyata ke aikin Hajji da kuma layya.

A wani labarin kuma mun tattaro muku Jerin gwamnoni huɗu da suka ɗauki tsauraran matakan kawo karshen yan bindiga a jihohin su

Yan ta'adda, yan fashin daji, yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran kashe-kashen masu aikata muggan laifuka na cigaba da hana zaman lafiya a wasu sassan Najeriya.

Sai dai wasu gwamnoni da lamarin ya shafi jihohin su, sun ɗauka matakai masu tsauri na ƙara wa jami'an tsaro ƙarfi, da ba jama'a damar kare kai da nufin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262