Yadda ake Istikhara a addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Bn Uthman

Yadda ake Istikhara a addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Bn Uthman

Sheikh Muhammad Bn Uthman, Malamin addini ne mazauni jihar kuma Limamin Masallacin Sahaba dake Kundila, Maiduguri Road, Kano.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

YADDA AKE SALLAR ISTIKHARA A SUNNAH

Daga Sheikh Muhammad Bn Uthman Kano

Neman zaɓin ALLAH, wata sallah ce mai raka'o'i biyu 2, wacce yinta sunnah ce mai ƙarfi.

Wacce Manzon ALLAH {s.a.w} ya koyar da sahabbansa ita har tazo garemu, kamar yadda Alƙur'ani ya iso gare mu, Sallace da akeyi, lokacin da ake neman zaɓin ALLAH akan wani al'amari kamar:

• Aure.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

• Sayan gida

• Mota

• Aikin gwabnati da dai sauransu

Sai dai ita wannan sallar ba'ayinta akan abinda yake wajibi ko mustahabbi akanka.

Kara karanta wannan

Babban ɗan shugaban Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya rasu

Kamar neman zaɓin ALLAH akanyin azumin Ramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitar da zakkah, ko azumin alhamis da litimin da dai sauransu.

Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan sunci karo, misali:

Mutum ne yake son yaje umrah karo na biyu, a lokaci guda kuma yana so yaje wata ƙasa neman ilimi, to yana iya neman zaɓin ALLAH akan ya zaɓa masa wanda yafi alkhairi a cikin su.

Haƙiƙa duk wanda ya nemi zaɓin Mahaliccinsa, kuma yayi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikin lamarin sa, to bazai yi nadama ba Insha ALLAH.

Domin ALLAH TA'ALAH yace:

Kuma ka shawarcesu cikin lamarinka, idan kuma kaƙuduri aniya, to ka dogara ga ALLAH [Ali-Imran :159].

Hadisi yazo daga Jabir ibn Abdullah, da Maihaifinsa (RA) yace:

Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance yana koya mana yin Istikhara (neman zaɓin ALLAH) acikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin surorin Alƙur'ani.

Kara karanta wannan

Hajji 2022: Wani Alhaji ɗan Najeriya ya maida makudan kuɗin da ya tsinta a jaka a Madinah

Yakance Idan ɗayanku yayi niyyar yin wani al'amari, to, yayi sallah raka'a biyu,

Sannan yace:

( Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika, wa'astaƙdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru, wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube,

Allahumma inkumta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibatiamrii, aajilihi wa'aajilihi faƙadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamu anna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu' anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaanathumma raddini bihi)

Ma'ana:

(Ya ALLAH ina neman zaɓinka da iliminka, kuma ina neman tabbatuwar ikonka, ina roƙan falalarka mai girma, Kai ke da iko ni banda shi, Kaine masani ni bansan komai ba, Kaine masanin abin da yake ɓoye. Ya UBANGIJI na, Inkana ganin wannan abu (sai mutum ya faɗi abinda yakeyin istikharan a kai)

Shi yafi min a addinina da rayuwata da ƙarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauƙaƙe min sannan kasamin albarka acikinsa,

Kara karanta wannan

Da alama guguwar sauya sheƙa ba ta lafa ba a APC, wani ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

In kuwa kana ganin wannan abu sharri ne gareni a addinina da rayuwata da ƙarshen lamarina, ka juyar dashi daga gareni, nima kajuyar dani daga gareshi, ka ƙudurtarmin da alkhairi sannan kamantar min dashi

[Bukhari]

• Ita dai wannan Sallah Mustahabbi ce anso kayita domin sunnah ce mai ƙarfi, sannan zaka samu lada idan kayi, amma idan bakayi babu laifi.

• Wannan Addu'a ta istikhara ana yin tane bayanka sallame sallar nan da kayi mai raka'a biyu,

Duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane bayan tahiya da salatin Manzon ALLAH {s.a.w} kafin Sallama, domin mafi alkhairin bijiro da addu'a acikin sallah shine acikin sujada da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.

ALLAH shine Mafi Sani..

Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakhara sama da ɗaya, hakam ya tabbata daga cikin magabata, kamar Abdullahi ɗan zubair (RA) yayi istakhara sau uku 3. [Muslum 970].

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An shiga Ruɗani da rashin tabbas kan batun Murabus ɗin shugaban Alƙalai na Najeriya

• Babu wani hadisi daya inganta da yazo da surorin da ake karantawa, a cikin sallar neman zaɓin ALLAH.

• Haka kuma babu wani hadisi da yazo daga Manzon ALLAH {s.a.w} cewa idan mutum yayi istakhara zaiyi mafarki ko zaiga wani mutum yana yi masa bayanin al'amarinsa.

• Babu shakka duk wanda yayi zai samu nutsuwa cikin abinda ALLAH maɗaukakin sarki ya zaɓa masa.

• Ba mafarki ake yiba kamar yadda mutane da yawa suka ɗauka, ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, Idan aure ne, sai kaji zuciyarka ta ƙara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka fara sai kaji zuciyar ka, ta nutsu da sana'ar.

• Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu, da rana ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita ne daga lokaci zuwa lokaci har sai ka sami biyan buƙata,

• Sannan anayin tane koda lokacin da aka hana yin sallah ne, idan buƙatar hakan ta taso, domin ita tana daga cikin Nawafilul Asbab - Nafiloli masu dalili.

Kara karanta wannan

2023: Zulum Muke So Ya Zama Mataimakin Tinubu, Masu Ruwa Da Tsaki Na APC

• Wannan kenan don gane da abunda ya shafi Sallar neman zaɓin AALLAH maɗaukakin Sarki,

• Baya halatta wani ga yiwa wani istikhara, duk wanda yace zaiyi maka istikhara to da alama shi ɗin Boka ne acikin rigar malanta.

Muna fatan ALLAH ya bamu damar aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya.

Ameen.

Allah yasa mudace ameen ya'Allah

•Sheikh bn uthmaan Kano

•mbn-Ahmad Rufai ✍️

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng