Da alama guguwar sauya sheƙa ba ta lafa ba a APC, wani ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

Da alama guguwar sauya sheƙa ba ta lafa ba a APC, wani ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

  • Guguwar sauya sheƙa na cigaba da ɗauke mambobin jam'iyyar APC yayin da ɗan takarar gwamnan Ogun ya fice daga jam'iyyar
  • Adekunle Akinlade ya bayyana cewa ba zai iya cigaba da zama a wurin da rashin adalci ya yi katutu ba, uwar jam'iyya ta ƙi yin komai
  • Ɗan takarar ya nemi zama gwamna a zaɓen 2019 amma ya sha ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APM daga bisani ya koma APC

Ogun - Ɗan takarar gwamnan jihar Ogun karkashin jam'iyyar APM a zaɓen 2019, Adekunle Akinlade, ya yi murabus daga kasancewarsa mamba a jam'iyyar APC, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Akinlade, wanda tsohon gwamnan Jihar, Ibikunle Amosun, ya zaɓo don ya gaje shi, ya fafata da gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun wajen neman tikitin APC a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

Adekunle Akinlade.
Da alama guguwar sauya sheƙa ba ta ƙafa ba a APC, wani ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Amma ya sha kaye a hannun Abiodun kuma ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) inda ya tsaya takara a zaɓen. Ya kuma sake dawo wa APC bayan rashin nasara a 2019.

Duk da haka bai hakura ba, tsohon mamba a majalisar wakilan tarayya wanda aka fi sani da 'Triple A' ya nemi takara a zaɓen fidda gwanin APC da ya gudana a watan Mayu, ya sake shan ƙasa hannun Abiodun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa ya ɗauki matakin barin APC?

A wasiƙar da ya aike wa shugaban APC na jiha, Akinlade ya alaƙanta dalilin ficewarsa da gazawar uwar jam'iyya na shiga tsakanin rikicin da ya ƙi ƙarewa a reshen jihar Ogun.

Premium times ta rahoto Wasikar ta ce:

"Ina mai sanar maka a hukumance cewa na yi murabus daga matsayin mamba a jam'iyyar APC. Don cika umarnin dokokin APC na kawo karshen zama mamba ina tabbatar da cewa babu wani abu ko kaya na jam'iyya da ke hannu na."

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya ɓarke a PDP, Babban Jigo ya yi watsi da Atiku, yace wajibi mulki ya koma kudu a 2023

"Hakan ya zama tilas a gare ni saboda gazawar uwar jam'iyyar na shiga tsakani domin warware rikicin cikin gida da ya baibaye reshenta a jihar Ogun. A matsayin mutum me manufa ba zan iya cigaba da zama inda ake kaucewa adalci ba."

A wani labarin kuma batun karɓa-karba ya dawo ɗanye a PDP, Fayose ya yi watsi da Atiku, ya ce wajibi mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023

Sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya PDP, tsohon gwamnan Ekiti ya yi hannun riga da tsayar da ɗan arewa a 2023.

Ayodele Fayose, ya ce tsarin mulkin PDP ya tanadi tsarin karɓa- karba, wajibi bayan Buhari a yi adalci, ɗan kudu ya karɓi shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel