Kada wanda ya fito yau, IPOB ta umarci yan jihohin Igbo
- IPOB ta umurci yan jihohin kudu da su zauna a gida yau Talata
- Wannan sanarwar tasu ta zo ne ganin cewa shugaban su Nnamdi Kanu ya bayyana a kotu yau
- Kungiyar tace dole kowani kabilar Igbo ya nuna wa Shugaban nasu goyan baya
Tsagerun kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ta umurci yan jihohin Igbo da kada su sake su fito yau Talata.
Mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, yace sun dauki matakin ne ganin cewa shugaban su Nnamdi Kanu ya bayyana a kotu yau Talata kamar yadda Jaridar Nation ta ruwaito.
zaman gida da suka kakaba wa mutane na ranar Litinin har yanzu ya sanya bankuna, kasuwanni, shaguna da sauran wasu harkoki na yau da kullum a Jihar Anambara da ma wasu jihohin a tasgu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fararen hula a Anambara basa iya fitowa su je Ofisoshinsu saboda barazana da yan kungiyar suke wa rayuwarsu.
A wani jawabi da kungiyar (IPOB) ta saki ranar Litinin, tace: " Mun riga a da mun bayyana cewa duk ranar da Shugaban mu Nnamdi Kanu zai bayyana a kotu to dole kowa ya nuna mishi goyon baya.
"Saboda haka, yau Talata ya zama dole ga kowani kabilar Igbo ya zauna a gida."
Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili
A wani labarin, Amb Ginika Tor ta yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da kada su yi kuskuren zaben jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.
Wakiliyar ta jihar Enugu a hukumar da’a ta tarayya ta ce jam’iyyar PDP ba ta cancanci kuri’un kabilun Igbo ba, saboda kin amincewar jam’iyyar na ba da tikitin takarar shugaban kasa a yankin kudu maso gabas, inji rahoton jaridar The Nation.
Ta ce a maimakon goyon bayan Atiku tare da kada masa kuri'u, ya kamata dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shahara ya kuma mamaye kuri'un yankin.
Asali: Legit.ng