Lalacewar tarbiyyar yara ne musabbabin matsalar tsaro a Najeriya, Gwamna Sanwo Olu, Sirika

Lalacewar tarbiyyar yara ne musabbabin matsalar tsaro a Najeriya, Gwamna Sanwo Olu, Sirika

  • Gwamnan Legas ya ce lokaci ya yi da kowa zai tashi tsaye wajen tabbatar da an ba yara kyakkyawar tarbiyya tun daga wurin iyayen su
  • A cewar gwamnan da kuma Hadi Siriki, lalacewar tarbiya ce asalin dalilin da ya jawo aikata manyan laifuka a Najeriya
  • Ministan sufurin jiragen sama ya ce duk masu aikata muggan laifukan nan sun fito ne daga rashin kula da tarbiyya mai kyau

Lagos - Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, da ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, sun ce ta hanyar ba da kyakkyawar tarbiya Najeriya zata iya rage yawaitar aikata manyan laifuka, garkuwa, ayyukan ƙungiyoyin asiri da sauran su.

Manyan mutanen biyu sun bayyana hanyar warware matsalolin ne a wurin babban taron ƙungiyar Ansaru-Ud-Deen Society of Nigeria karo na 10, wanda ya gudana a Legas, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamfara: CDS Irabor ya Kalubalanci Umarnin Gwamna ga 'Yan Jihar na Mallakar Makamai

Gwamnan jihar Legas da Hadi Sirika.
Lalacewar tarbiyyar yara ne musabbabin matsalar tsaro a Najeriya, Gwamna Sanwo Olu, Sirika Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Batun da taron ya maida hankali a wannan karon shi ne, "Tarbiyya da kuma yadda rashin kirki, rashin tsaro, taɓarɓarewar tattalin arziki ke shafar ƙasa."

Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas, ya ce gazawar iyalai a matsayin matakin farko na ba da tarbiya na ɗaya ɗaga cikin dalilian da suka jawo kalubalen da ake fama da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar gwamnan, lokaci ya yi da kowa zai tashi tsaye wajen tabbatar da cewa Iyalai sun san matsayin su tare da sauke nauyin da ke kansu na kula da yara da ɗora su kan hanya mai kyau.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kwamishinan gidaje, Moruf Akinderu-Fatai, ya koka kan yadda iyaye suka daina zama a gida su kula da yaran su yadda ake tsammani.

Maimakom haka sai suka bar ƴaƴan su suna yanke wa kansu hukuncin da zai shafi tsarin rayuwarsu, inji gwamnan.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

Dole iyaye su kula da yaran su - Hadi Sirika

A na shi ɓangaren Hadi Sirika, wanda ya gudanar da Lacka a wurin, ya ce wajibi iyaye su matsa wajen koya wa yara kyawawan halaye domin gina al'umma nagari da zasu guji aikata laifuka.

Ministan, wanda shugadan Ansaru-Ud-Deen, AbdulRahaman Ahmad, ya wakilta ya ce duk waɗan nan masu aikata ta'addancin sun samo asali ne daga rashin tarbiyya.

A wani labarin kuma An shiga Ruɗani da rashin tabbas kan batun Murabus ɗin shugaban Alƙalai na Najeriya

An shiga ruɗani da rashin makama kan harkokin sashin shari'a masu alaƙa da ofishin shugaban alƙalan Najeriya (CJN), kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Yayin da rahotanni ke yawo cewa Alkalin Alkalai na ƙasa, CJN Tanko Muhammad, ya miƙa takardar murabus daga kan mukaminsa, hukumomin shari'a sun ƙi cewa komai kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: