Zargin Cire Sassan Jikin Mutum: Sanatoci Suna 'Tare Da Ekweremadu', In Ji Smart Adeyemi
- Sanata Smart Adeyemi, dan majalisar dattawar Najeriya daga Jihar Kogi ya ce sanatoci na tare takwararsu Ike Ekweremadu
- Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tsokaci kan batun tuhumar da aka yi wa Ekweremadu na cire sassan jikin mutum a Birtaniya
- Sanata Adeyemi ya ce ya san Ekweremadu a matsayin mutumin kirki don haka ba za su watsi da shi ba a yanzu amma suna kokarin sanin cikaken bayani
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Dan majalisar tarayyar Najeriya, Sanata Smart Adeyemi ya ce sanatoci ba za su yi watsi da Sanata Ike Ekweremadu ba kuma wasu cikinsu na kokarin tuntubarsa.
Yana martani ne kan zargin cire sassan jikin mutum da aka yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan sanda a Birtaniya, a ranar Alhamis sun kama tare da gurfanar da Sanata Ekweremadu da matarsa kan zarginsu da hadin baki don kawo yaro Birtaniya da nufin cire sassan jikinsa.
Da ya ke magana da Channels Television, Sanata Adeyemi wanda ya ce har yanzu akwai abubuwa da ba a sani ba game da tuhumar ya ce ya kamata a yi taka tsan-tsan ba a yi saurin sukar Sanata Ekweremadu ba.
Ya ce idan an samu karin bayani game da batun amincewa ba, zai yi wuya a iya bada ra'ayi mai kyau kan batun.
"Abin babu dadi," Adeyemi ya shaidawa Channels Television. "Abin damuwa ne ga kowa a Majalisa domin takwarar mu ne; mafi muhimmanci don na san shi mutumin kirki ne; mai hali na gari.
"Bayan hakan, ina a halin yanzu anyi gaggawa idan aka bada laifi ko akasin hakan. Dukkan mu abokan aiki ne, mun jin zafin abin kuma muna tare da Ike Ekweremadu a kan wannan. Ba za mu yi watsi da shi ba.
"Wasu cikin sanatoci sunyi kokarin tuntubarsa domin ganin abin da za mu iya yi don taimaka masa ko karfafa masa zuciya.
"Amma muna son sanin cikaken bayani. Batun shine wanda abin ya faru da shi bai kai 18 ba, don haka ake ganin ba shi da hurumin yanke hukuncin zai bawa wani sassan jikinsa."
Safarar Sassan Jikin Mutum: Za A Iya Yi Wa Ekweremadu Da Matarsa Daurin Rai Da Rai A Birtaniya
Tunda farko, kun ji ana iya yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice daurin rai da rai idan aka same su da laifi kuma aka yanke musu hukunci mafi tsauri a dokar Birtaniya ta Modern Slavery Act, 2015 (MSA 2015).
An kama mata da mijin ne aka kuma gurfanar da su a kotun Birtaniya kan zargin hannu cikin cire sassan dan adam a kotun Majistare da ke Uxbridge a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng