Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

  • A ranar Laraba, wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne sun tasarwa sansanin sojin kasan jihar Borno a kauyen Ajire inda suka tarwatsa dakarun
  • Tsananin luguden wutar da suka musu ne ya tilasta sojin tserewa gami da watsi da kayyakin aikinsu da muhimman makamansu
  • Kamar yadda aka gano, 'yan bindigan basu taba wani daga cikin mazauna yankin ba, sai dai sun tattara muhimman abubuwa sojin gami da yin awon gaba dasu

Borno - Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan ISWAP ne, sun kai wa sansanin sojoji farmaki a daren Laraba a jihar Borno.

Daily Trust ta gano yadda hatsabiban suka kai wa dakarun hari a kauyen Ajire cikin karamar hukumar Mafa misalin karfe 9:00 na dare, wanda hakan ya tilasta sojin ranta a na kare ba tare da wata kwakwkwarar musayar wuta ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Taswirar jihar Borno
Borno: 'Yan Ta'addan Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Majiya ta bayyana yadda kimanin soji 80 a sansanin suka tsere, tare da barin wasu makamai da kayayyakin da suka hada da wayoyi, wanda hatsabiban suka yi awon gaba dasu.

An ruwaito yadda sojojin suka gaza yin fito na fito da 'yan bindigan saboda rashin carbin harsasai da kayan yaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"'Yan ta'addan sun fatattaki dakarun sojin Najeriya da aka bari da tsirarun carbin harsasai kuma ba tare da kayayyakin da za su kare kansu irin su RPG, AA da MG," a cewar majiyar.

Mazauna yankin sun bayyana yadda 'yan ta'addan suka kai farmaki kauyen Ajire tsakanin karfe 9:00 na dare zuwa karfe 4:00 na yammacin Alhamis, sai dai basu hari mutanen yankin ba, amma an ga yadda suke tattara muhimman abubuwa a sansanin sojojin.

Al’ummar jihar Neja sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya da yan bindiga

Kara karanta wannan

Ana shirin yin waje da duk wani Sojan da ba a gama yarda da imaninsa ba a Najeriya

A wani labari na daban, mazauna yankunan da ta'addancin 'yan bindiga yayi kamari a yankin Kusherki na karamar hukumar Rafi ta jihar Niger sun nemi zaman lafiya da 'yan bindiga.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindigan suka bukaci a yi yarjejeniyar zaman lafiya da mazauna yankin tare da sharadin cewa ba zasu dinga kai su kara wurin hukuma ba duk lokacin da suka ketare yankunansu.

Shugaban yankin Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya sanar da Daily Trust cewa tuni suka tura wakilai domin tattaunawa da 'yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng