Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirinsa na ragargazar masu ta da hankalin jama'a a kasar nan
- Shugaban ya bayyana cewa, akwai miyagu da ke amfani da sunan addini da siyasa domin haifar da hargitsi a kasar
- Ya kuma bayyana cewa, Najeriya ba za ta samu rabuwar kai saboda wasu bata-gari da ke son ganin bayanta ba
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ce hare-haren da aka kai wa coci-coci cikin kwanaki 14 ya nuna cewa akwai wani shiri da miyagun mutane suka yi domin jefa Najeriya cikin damuwa ta addini.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya naqalto Buhari yana fadar haka a cikin wata sanarwa mai taken ‘Ba ji dadin Hare-haren Coci a ‘yan kwanakin nan ba.'
Buhari ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen yin addu’a tare da rike wadanda abin ya shafa da iyalansu a cikin zukatansu da tunaninsu, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda suka kai hare-haren a gaban kuliya, ya kuma bukaci dukkan ‘yan Najeriya su sani cewa, duk wani mugu muguntarsa za ta dawo kansa ya daidaice.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaba Buhari na mayar da martani ne kan iftila'in ta'adanci da ya faru a garin Owo na jihar Ondo makonni biyu da suka gabata da kuma kashe-kashe da sace-sacen da aka yi a Kaduna.
Da yake bayyana shirin daukar mataki, shugaban ya ce:
“Ba za mu kyale su ba. Al’umma ba za ta wargaje ko ta rabe saboda wadannan munanan laifuka da ake shiryawa a fili a siyasance ba."
Daya daga cikin 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH
A wani labarin, shekaru takwas bayan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata 276 a makarantar Sakandaren Chibok a Borno, rundunar sojin Operation Hadin Kai ta ceto wasu karin ‘yan matan Chibok biyu a dajin Sambisa.
An ce rundunar ta ceto su ne a yankin Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno a kwanan baya. Wadanda aka kubutar din su ne Mariam Dauda da Hauwa Joseph ne tare da jariransu, Daily Trust ta ruwaito.
Bayan ceto su sun ba da labarin wahalar da suka sha na tsawon shekaru takwas a cikin dajin a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban dakin taro na Command-and-Control Center da ke Maimalari a Maiduguri ranar Talata.
Asali: Legit.ng