Borno: An Fallasa Dabarju, Mai Tatsar Wutar Fitillun Kan Titi Yana Kaiwa Gidan Kankararsa
- Mazauna GRA Maiduguri sun fallasa wani mai gidan Kankara dake tatsar wuta daga janareton gwamnatin jihar
- An gano cewa, Dabarju ya yi dabara inda yake tatsar wutar daga fitillun kan titi wadanda janareton gwamnati ke bai wa wuta
- A cewar wasu, ya kwashe shekaru 2 zuwa 3 yana satar wutar, kuma da aka gano shi yayi tayin cin hancin N1 miliyan
Maiduguri, Borno - Mazauna yankin GRA Maiduguri a ranar Talata sun fallasa wani mutum da ake kira da Dabarju kan satar wutar lantarki daga janareton gwamnati da ake amfani da shi wurin bai wa fitillun kan tituna haske.
Dabarju dai ya mallaki gidan kankara kuma ana zarginsa da tatsar wuta daga janareton gwamnatin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sakataren GIS na jihar Borno, Adam Bababe ya jagoranci tawaga wacce ta rushe gini ba bisa ka'ida ba da Dabarju yayi.
Tawagar ta kara da kwashe kusan firji 20 da ake amfani da su a gidan kankarar inda tace an dade ana wannan aika-aikar.
"Wasu sun ce shekaru biyu, wasu sun ce uku amma muna cikin bincike ne a yanzu."
Bababe yace lamarin ya janyo gagarumin Lodi wanda ya kawo lalacewar janaretoci har biyu da ake amfani da su wurin bai wa fitillun kan titin GRA din wuta.
Ya yaba wa wasu mutanen kirki da suka fallasa wanda ake zargin wanda a halin yanzu yana hannun jami'an hukumad NSCDC, Vanguard ta ruwaito.
Ya yi kira ga jama'a da su cigaba da fallasa masu irin wannan dabi'ar ta zagon kasa ga kokarin gwamnati.
Wasu mazauna yankin da suka tofa albarkacin bakinsu kan wannan cigaban, sun nuna mamakinsu kan wannan abu inda suka ce sun dade suna mamakin inda gidan kankarar ke samo wutar lantarki tunda an san Maiduguri ta dade tana fama da rashin wuta.
Mohammed Al-Amin, daya daga cikin wadanda suka fallasa Dabarju, ya yi ikirarin cewa mutumin ya yi masa tayin cin hancin miliyan daya idan ya yi shiru amma ya ki amincewa.
"Ni na fara gano abinda yayi kuma yace zai bani cin hancin miliyan daya amma na ki karba," Al-Amin yace.
Wutar Lantarkin Najeriya ta Lalace, Daga 3,703MW An Koma Samun 9MW, FG
A wani labari na daban, a ranar Litinin, Bangaren tsarin samar da wutar lantarki ta Najeriya, wani sashi na kamfanin rarrabe wutar lantarki na gwamnatin tarayya, ya nuna cewa wutar lantarkin kasar nan ta lalace a ranar Lahadi inda ta koma samar da wuta mai yawan 9MW daga 3,703MW.
Najeriya tana fuskantar rashin wutar lantarki tun daga ranar Lahadi bayan wutar ta lalace wurin karfe 6 na yammaci, kafin injiniyoyin Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki na Najeriya su yi kokarin farfado da ita.
Asali: Legit.ng