Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki wani yankin jihar Kaduna
  • An tattaro cewa, sun hallaka wasu mutane a coci kana suka sace wasu bayan sace ababen hawa da kayayyaki
  • Ya zuwa yanzu, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ta Kaduna ya yi tattaki zuwa yankin domin jajantawa da nemo mafita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kajuru, jihar Kaduna - Akalla mutane 36 ne aka ruwaito an yi garkuwa da su a wani harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna ranar Lahadi.

Mazauna kauyukan ne suka bayyana hakan a wata ganawa da jami’an tsaro a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito.

Mazauna yankin sun ce hare-haren da ake kai wa a kai a kai ya shafi rayuwarsu, domin ba za su iya zuwa gonakinsu ba a halin yanzu don gudun kada ‘yan bindiga su kashe su.

Kara karanta wannan

ISWAP Ta Halaka Rayuka 16, Ta yi Garkuwa da Ma'aikatan Tallafi 3 a Borno

'Yan bindiga sun yi sabon barna a Kaduna
Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutum 36 | thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sun kuma ce suna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Kajuru domin ita kadai ce hanyar da za a magance matsalar tsaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani ganau kuma mazaunin kauyen Kufana, Bashir Bawo, ya bayyana cewa:

“Sa’ad da suka zo, suka hadu da wasu mutane a cikin coci; sai suka yanke shawarar shiga cocin, suka kwashe wasu daga cikinsu, suka tattara su a wani wuri, suka tafi wani kauye."

A cewarsa, ‘yan bindigan sun zo ne a kan babura inda suka kara sace babura daga mutanen kauyen domin su tafi da wasu mutane. Ya ce sun kashe wasu daga cikin mutanen kauyen da suka yi kokarin dakile harin kana sun jikkata wasu, rahoton This Day.

Gwamnatin ta kai ziyarar duba Kufana

Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a ranar Litinin, ya jagoranci jami’an tsaro zuwa gundumar Kufana domin samun cikakken bayani game da harin tare da tattaunawa da jama’ar kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari karamar hukumar gwamnan Bauchi

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Yekini Ayoku, da sauran shugabannin hukumomin tsaro na jihar, da shugabannin al’umma, da shugaban karamar hukumar Kajuru.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan ta’addan suka kai hari kan wasu al’ummomi hudu inda suka kashe wasu masu ibada uku daga coci guda biyu tare da kwashe wasu mazauna wurin.

An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

A wani labarin, a ranar Lahadi ne wasu ‘yan daba suka far ma motar bas din da ke dauke da ma’aikatan ofishin gwamnan jihar Legas a tsakanin Ebute-Ero da Adeniji, na yankin Iga-Iduganran a Legas, inda ‘yan jarida akalla biyu suka samu raunuka, wasu kuma suka kuje a jikinsu.

'Yan daba sun afkawa 'yan jaridan ne da ke cikin ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

An rahoto cewa, tsagerun sun kuma jefi motocin da ke cikin ayarin da ya kunshi jiga-jigan siyasa ciki har da Gwamna Babajide Sanwo-Olu; Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje; da sauran wadanda suka bar fadar Oba na Legas, Oba Rilwanu Akiolu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.