Wata sabuwa: Gwamnatin Najeriya ta kuduri kawar da amfani da kananzir nan da 2030
- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana shirin da ake yi na hana amfani da kananzir a kasar daga shekara ta 2030
- Hakan na daga kokarin gwamnatin tarayya na dakile gurbatar yanayi, za ta kuma habaka amfani da iskar gas
- Shugaba Buhari ne ya bayyanawa shugaban kasar Amurka Joe Biden hakan a wata tattaunawar yanar gizo
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, za a yi mai yiwuwa domin ganin 'yan Najeriya sun daina amfani da makamashin kananzir da itacen girki daga 2030.
A cewar Buhari, wannan wani bangare ne na tsare-tsaren gwamnatinsa na rage azababben hayaki mai gurbata muhalli, inji Punch.
Ya kara da cewa an mika hukumar NDC mai alhakin kula da aikin ne domin maye gurbin gudunmawar wucin gadi na ranar 27 ga Mayun bara; 2021 tsakanin Najeriya da majalisar dinkin Duniya.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadimin kan yada labarai, Femi Adesina ya sanyawa hannu, kuma manema labarai suka samu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar ta Adesina ta ce, Buhari ya bayyana wadannan zantuka ne a yayin wata ganawar bidiyo da shugaban kasar Amurka, Joe Biden.
Buhari ya ce gwamnati za ta tabbatar da maye gurbin kananzir da itace da iskar gas na girki don rage gurbatar yanayi da iska a kasar, Punch ta ruwaito.
Hakazalika, shugaban ya kuma yi tsokaci ga yadda kasashen duniya ke raja'a ga amfani da wasu abubuwan daban ba kananzir da itace ba, inda ya ce yana fatan Najeriya ta yi gogayya da sauran kasashen na duniya nan da 2023.
Wani yanki na sanarwar na cewa:
“Gwamnatin Najeriya na sane daram da cewa yawan dogaro da makamashi mai hayaki na jefa kasar cikin barazana a yayin da kasashen duniya ke kokarin daina amfani da shi a matsayin abin dogaro ga tattalin arzikinsu.”
A bangare guda, shugaban ya bayyana kyakkyawan hasashen amfani da motocin bas a kasar a matsayin ababen sufuri, duk dai don rage gurbatar yanayin iska a Najeriya.
Rahotanni a shekarun baya tun 2012 sun bayyana hobbasan da gwamnatin Najeriya ke yi don ganin an rage amfani da kananzir da itace, domin illar da ke tattare dasu da kuma maye su da iskar gas, rahoton Tribune.
Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya taya dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin inuwar Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Biodun Oyebanji, murnar lashe zaben da ya yi.
Shugaban kasar ya kuma taya shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da kwamitin aiki na jam’iyyar murna kan wannan nasara wanda ita ce ta farko a karkashin sabuwar shugabancin jam’iyyar.
Asali: Legit.ng