Labari Da Duminsa: Farfesa Soyinka Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Labari Da Duminsa: Farfesa Soyinka Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Farfesa Femi Soyinka, farfesa masanin ilimin cutukan fata da garkuwar jiki, ya rasu a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo
  • Kamar yadda takardar da 'dansa ya sa hannu kuma ta fita a madadin iyalan, ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata, 14 ga watan Yuni
  • Duk da likita ne, ya yi aiki na tsawon shekaru 30 yana kjoyarwa kuma ya bada gudumawa wurin binciken cutukan fata

Oyo - Farfesa Femi Soyinka, Farfesa masanin likitancin fata da garkuwar jiki, ya rasu. Kanin fitaccen marubucin nan ne na Afrika, Farfesa Wole Soyinka ne.

Kamar yadda takardar da iyalan Soyinka na Ake/Isara a jihar Ogun suka fitar, Farfesa Soyinka ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata, 14 ga Yunin 2022 a gidansa sa ke kauyen Kukumada na farin Ibadan, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sojoji sun gano wata mata da Boko Haram suka sace tun 2014

Takardar ta samu sa hannun 'dan shi mai suna Ayodele a madadin iyalan, jaridar Leadership ta ruwaito.

Farfesa Femi Soyinka, Likita Masanin Cutukan Fata Da Ilimin Garkuwar Jiki
Labari Da Duminsa: Farfesa Soyinka Ya Rigamu Gidan Gaskiya. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

An haifa Farfesa Femi Soyinka a 1937. Ya samu digiri na farko a fannin likitanci a shekarar 1964 daga jami'ar Heidelberg kuma ya samu digiri na biyu daga jami'ar a shekarar 1965. Ya kware tare da aiki amatsayin likitan fata a jami'a Giessen a shekarar 1969.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A 1972, ya kammala digiri na biyu a fannin lafiyar al'umma daga makarantar likitanci ta Hadassah dake Israel.

Ya yi aikin koyarwa na tsawon sheka 30 inda ya rike mukamai daban-daban da suka hada da babban daakta asibiti zuwa shugaban sashin karatun lafiya da shugaban kwalejin lafiya na jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Najeriya.

Ya mayar da hankali wurin bincike kan cutukan fata da kuma STIs tare d hadn guiwa gwamnatin tarayya da kungiyoyi kamar su bankin duniya, UNDP, DFID da sauansu.

Kara karanta wannan

Fitaccen Farfesa na BUK, Emmanuel Ajayi Olofin, ya Riga mu Gidan Gaskiya

Shi ya fara bincike a bangaren cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS.

Fitaccen Farfesa na BUK, Emmanuel Ajayi Olofin, ya Riga mu Gidan Gaskiya

A wani labari na daban, wani fitaccen Farfesan ilimin Jogirafi a jami'ar Bayero dake Kano (BUK), Emmanuel Ajayi Olofin ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin, 'dan asalin Ijero cikin jihar Ekiti ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 80, Daily Trust ta ruwaito.

Kafin mutuwarsa, Olafin ya koyar a fannin jogirafi a BUK, inda ya kai kololuwa a fannin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel