ISWAP Ta Halaka Rayuka 16, Ta yi Garkuwa da Ma'aikatan Tallafi 3 a Borno
- Rayuka a kalla 16 ne suka salwanta bayan mayakan ta'addanci na ISWAP sun kai mummunan farmaki jihar Borno
- An gano cewa, 'yan ta'adfdan sun shiga kauyen Goni Kurmi dake karamar hukumar Bama inda suka halaka 'yan gongon 13 a take
- 'yan ta'addan sun kara kai farmaki har garin Monguno inda suka kashe jami'an CJTF 3 tare da sace ma'aikatan tallafi 3
Borno - A kalla rayuka 16 da suka hada da jami'an tsaron hadin guiwa na farar hula suka rasa rayukansu a hare-haren da mayakan da ake zargin 'yan ISWAP ne suka kai Borno, majiyoyi suka tabbatar.
An tattaro cewa, 'yan gongon 13 ne mayakan ta'addancin ISWAP suka harbe a kauyen Goni Kurmi dake karamar hukumar Bama ta jihar a anar Asabar da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.
Jami'an sirri sun sanar da Zagazola Makama, kwararre a harkar yaki da ta'addanci kuma mai kiyasin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa, wadanda aka halaka din sun hada da maza 11 sai mata biyu.
Yace mayakan da suka bayyana a ababen hawa har hudu da wasu kuma a kan babura, sun zagaye yankin yayin da suka dinga cin karensu babu babbaka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyoyi sun tabbatar da cewa, mutane masu tarin yawa sun dinga gudun ceto rayukansu.
Har ila yau, mambobin CJTF uku sun rasa rayukansu yayin da wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne suka kai musu farmaki tare da sace masu aikin tallafi 3 a arewacin jihar Borno a ranar Juma'a.
Lamarin ya auku ne a karamar hukumar Monguno ta jihar Borno a daren Juma'a.
An tattaro cewa, maharan da suka tsinkayi kauyen ta yankin Marte, sun shiga ta Gana Ari dake Monguno kuma kai tsaye suka tafi gidajen ma'aikatan tallafin inda suka fara harbi babu kakkautawa. Sun raunata mutum daya a take.
"Sun yi yunkurin sace wasu ababen hawa uku amma sun kasa fitar dasu daga yankin. Daga bisani sai suka sace ma'aikatan tallafin uku tare da barin gidan," majiyar tace.
Idan za a tuna, sama da 'yan gongon 60 ne 'yan ta'adda suka halaka a kauyen Modu dake kananan hukumomin Kala-Balge da Dikwa a jihar Borno a makonni hudu da suka gabata.
Har a lokacin rubuta wannan rahoton, rundunar sojin Najeriya bata riga ta fitar da wata takarda kan farmakin ba.
Borno: Hotunan Tubabbun 'Yan Boko Haram 204 Yayin da Suka Mika Kansu ga Sojoji
A wani labari na daban, sakamakon tsananta ragargaza da ruwan wuta da rundunar sojin Najeriya ke yi wa 'yan ta'adda domin kawo karshen ta'addanci, ana ta samun manyan nasarori masu yawa.
Kamar yadda hedkwatar rundunar sojin kasa ta najeriya ta bayyana, ana samun nasara wacce aka kara samu a ranar 15 ga watan Yunin 2022.
Mayakan ta'adanci na Boko Haram har su 204 ne suka yadda makamai tare da mika wuya ga sojojin Najeriya.
'Yan ta'addan tare da iyalansu sun garzaya har karamar hukumar bama ta jihar Borno inda suka mika wuya ga sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng