Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su

Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya koka kan cewa ya gaza kare mutanen jiharsa a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni
  • Akeredolu ya bayyana hakan ne a cocin Katolika na Saint Francis da ke Owo, jihar Ondo a yayin bikin binne wadanda harin ya ritsa da su
  • Sai dai ya ce ba wai basu kokarta wajen aikata hakan bane, maharan ne basu da imani kuma suna da goyon baya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Hawaye sun kwaranya yayin da aka binne mutanen da harin ta’addanci ya cika da su a cocin Katolika na Saint Francis da ke unguwar Owaluwa, karamar hukumar Owo, jihar Ondo.

Gwamna Rotimi Akeredolu, wanda ya kasance tare da matarsa, Betty Anyanwu, a wajen, ya zubar da hawaye a yayin da yake jawabi, yana mai cewa sun gaza kare mutanen da harin ya ritsa da su, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Gwamnan jihar Ondo a wajen jana'izar mutanen da harin Owo ya ritsa da su
Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su
Asali: UGC

Ya bayyana cewa tawagar da ke daya gefen miyagu ne, yana mai tabbatar da cewa ba za su yi nasara ba har abada.

Kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun gaza kare wadannan mutane. Ba wai don bamu kokarta bane, amma wadannan tawagogin da ke daya defen miyagu ne kuma suna da goyon baya.

“Ba za su taba nasara ba a kanmu har abadah.”

Gwamnan ya bayyana cewa ya zama dole ayi wani abu a kasar nan, yana mai cewa tsarin tsaron kasar na bukatar gyara.

Ya ce:

“Da na ga yawan kawunan da ke nan; ya kare magana. Abin da ya faru da mu a garin Owo da ke jihar Ondo ba zai misaltu ba.

"Ana amfani da kalmomi da yawa don sifanta shi, mugunta, abun tsoro. Amma har yanzu ina ganin cewa akwai kalmomin da za ayi amfani da su don siffanta sh, sai dai har yanzu na gagara amfani da wadannan kalmomin.

Kara karanta wannan

To ka ji: ‘Dan takaran APC ya fadi dalilin janyewa Bola Tinubu takarar shugaban kasa

“Muna da mamata 22 ne kawai a wannan dakin. An binne yan kadan daga cikinsu saboda yan uwansu ba za su iya jira har zuwa yau ba. Amma a lissafin karshe, wadannan dabbobin sun zo cocin sannan suka kashe mutane 40.”

Sai dai kuma, da yake martani, babban faston cocin Katolika na Ondo, Dr. Jude Arogundade, ya ayyana cewa Gwamna Akeredolu bai gaza ba a wajen kare mutanensa.

Bishop Arogundade ya ce:

“Ba ka gaza ba. Kai soja ne mai karfi. Babu shakku a cikin jajircewarka don kare wadanda suka zabe ka kan mulki. Matsorata ne suka aikata haka. Ka yi iya bakin kokarinka.”

Ga bidiyon jana'izar da Legit.ng ta yi kai tsaye.

Harin cocin Ondo: Atiku ya bayar da gudunmawar miliyan N10 ga wadanda abun ya ritsa da su

A baya mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 10 ga wadanda harin ta’addanci ya cika da su a cocin Katolika na Owo da ke jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Yayin da ya kai ziyarar jaje ga masarautar Owo, Atiku ya yi Allah wadai da kisan masu ibadah da aka yi a ranar 5 ga watan Yuni, jaridar Vanguard ta rahoto.

Atiku ya samu wakilcin dan takarar kujerar gwamna na PDP a zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi, Eyitayo Jegede (SAN) da mambobin kwamitin aiki na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng