EFCC: Yan Najeriya Sun Dena Kazar-kazar Wurin Tona Asirin Masu 'Sata' Duk La'ada Mai Tsoka Da Muke Basu

EFCC: Yan Najeriya Sun Dena Kazar-kazar Wurin Tona Asirin Masu 'Sata' Duk La'ada Mai Tsoka Da Muke Basu

  • Mr Abdullahi Bawa, Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ya koka kan yadda yan Najeriya suka dena tona asirin masu tona asirin
  • Bawa ya ce duk cewa wadanda suka tona asirin a baya sun samu la'ada mai tsoka, bisa alamu yan Najeriya suna nesa-nesa da tsarin
  • Shugaban na hukumar yaki da rashawar ya ce akwai bukatar a zaburar da yan Najeriya su rika taimakawa hukumomin tsaro da bayanan sirri

Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta nuna rashin jin dadinta kan yadda yan Najeriya ke nuna halin ko in kula ga tsarin tona asirin masu laifi da Gwamnatin Tarayya ta kaddamar duk da lada da ake biya, rahoton Daily Trust.

Shugaban EFCC na kasa, Abdullahi Bawa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin wani taron jin ra'ayin al'umma na kwana guda kan karfafa masu ruwa da tsaki a kan tsarin tona asirin masu laifi da aka yi a Ilorin, Jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku: 'Zunuban' Wike, Dalilan Da Yasa Aka Zabi Okowa, Majiya Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Abdullahi Bawa, Shugaban EFCC.
EFCC: Yan Najeriya Sun Dena Kazarkazar Wurin Tona Asirin Masu 'Sata' Duk Lada Da Muke Basu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

An shirya taron ne da hadin gwiwa da Cibiyar Ilimin Watsa Labarai da Sadarwa, AFRICMIL, da gudunmawar gidauniyar MacArthur.

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Manyan kudaden da aka gano karkashin shirin sune $9.8m daga tsohon manajan NNPC, Mr Andrew Yakubu, da $11m daga wani gida a Osborne Towers, Ikoyi Legas.
"Yadda al'umma suke janye kafa daga shirin abin mamaki ne duba da cewa an biya la'ada mai tsoka ga wadanda suka fara rungumar shirin."

Bawa, wanda ya samu wakilcin Direktan Sashin Hulda da Al'umma EFCC, Osita Nwajah, ya ce akwai bukatar wayar da kan al'umma su cigaba da bawa hukumomin tsaro bayanai masu amfani.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164