Yau ce ranar karshen mika sunayen yan takaran shugaban kasa, INEC tace ba zata kara wa'adi ba

Yau ce ranar karshen mika sunayen yan takaran shugaban kasa, INEC tace ba zata kara wa'adi ba

  • Yayin da wa'adi ya kusan cika, hukumar INEC ta bayyana cewa ba zata kara wa'adi ko minti guda ba
  • Duk dan takarar da bai mika sunanansa da na abokin takararsa na iya rasa tikitin takara a zaben shugaban kasa
  • Jam'iyyar PDP ta bayyana sunan wanda zai yi takara da Atiku amma ba'aji daga wajen APC ba har yanzu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar gudanar da zabe a ranar Alhamis ta jaddada cewa ba za'a kara wa'adin da ta baiwa jam'iyyun siyasa ba na mika sunayen yan takarar kujerar shugaban kasa da mataimakansu.

Sakataren yada labaran shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanmi, a hirar da yayi da yan jarida ya bayyana cewa hukumar ba zata kara wa'adi ba.

Mai magana da yawun shugaban INEC yace:

"Zamu jira zuwa karfe 6 na yamma. Ba za'a kara wa'adi ba."

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Zaku tuna cewa INEC ta bayyana ranar karshe ga jam'iyyun siyasa na mika mata takaran shugaban kasa da mataimakansu.

Hukumar tace nan da ranar Juma'a, 17 ga watan Yuni misalin karfe 6 na yamma, za'a rufe karbar sunan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma na gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, an basu nan da ranar 15 ga watan Yuli, 2022.

INEC Charman
Yau ne ranar karshen mika sunayen yan takaran shugaban kasa, INEC tace ba zata kara wa'adi ba Hoto: @inec
Asali: Twitter

Jam'iyyun da suka bayyana mataimakan shugabansu

A ranar Alhamis, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana Gwamnan jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa, matsayin abokin tafiyarsa.

Kawo karfe 9:50 na daren Alhamis, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, bai sanar da nasa abokin tafiyarsa.

Rahotanni sun nuna cewa Tinubu ya gabatar da sunan wani dan jihar Katsina, Alhaji Kabir Ibrahim Masari, kafin ya gama yanke shawara sai a canza sunan.

Kara karanta wannan

Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023

Majiyoyi a sansanin Tinubu da Masari sun tabbatar wa Daily Trust haka ne a yammacin ranar Alhamis.

Dan siyasar da aka fitar din ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina.

Kuma an ce dan uwan Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina na yanzu ne.

Hakazalika, ya taba zama sakataren walwala na jam’iyya mai mulki a zamanin Kwamared Adams Oshiomhole a matsayin shugaban APC na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng