Hausa game duniya: WhatsApp ya inganta zubinsa, ya zabi Hausa cikin jerin harasansa
- Harshen Hausa ya kara shiga jerin harasan duniya sanannu, yayin da WhatsApp ya zabe shi ya zama yaren amfani a manhajar
- Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da WhatsApp ta fitar ta shafin Twitter a jiya Larana 15 ga watan Yuni
- Baya ga Hausa, sanarwar ta ambaci wasu manyan harasa biyu da za su yi amfani akan manhajar cikin sauki
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Daya daga cikin manyan harsunan nahiyar Afrika, kuma fitacce a duniya; Hausa, ya shiga jerin harasan da ake amfani dasu dungurungum a kan manhajar sada zumunta da hira ta WhatsApp.
Harshen Hausa dai a kullum na kara shiga duniya, inda kamfanoni da ma'aikatu ke amfani dashi wajen sadarwa.
A wannan karon, wani rubutu da manhajar ta WhatsApp ta yada a shafin Twitter ta ce, ta yi karin harasa uku na duniya wadanda daya daga ciki shine Hausa. Sauran biyun su ne Amharic da Oromo.
Bidiyo: Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurni An Nuna Alat Din Albashinsa Na Watan Mayu a Talabijin
Ya zuwa shekarar 2021, wata makala da ta Wikipedia ta kawo cewa, akwai akalla mutane 50,000,000 da ke magana da harshen na Hausa a duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Harshen Amharic harshe ne da galibi mutanen kasar Habasha ke magana da kuma rubutu dashi, wanda aka rahoto cewa, akalla akwai mutane 32,000,000 da ke tutiya da yaren.
A bangaren Oromo, kusan mutane 37,400,000 ke magana dashi, wanda ya sanya shi cikin hasara mafi shahara a duniya, kuma shi ma dai tushensa kasar ta Habasha ne.
Sanarwar da WhatsApp ta cire ya ce:
"A kan Android, yanzu kuna iya zabar harshen Amharic, Oromo, ko Hausa a matsayin yaren WhatsApp din ku."
Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki
A baya can, tsarin dandamali aike sakon nan take na yanar gizo, Telegram, ya maye gurbin Facebook cikin sauri har ma da dandamali WhatsApp da Messenger, bayan da aka samu barakar da ta sa manhajojin suka daina aiki.
Wata Kasar Afirka Ta Sha Gaban Najeriya a Matsayin Kasa Da Ke Kan Gaba Wajen Hako Danyen Mai a Afirka
Kamar Facebook da dandamali masu alaka da shi, Telegram ma na ba da damar kiran bidiyo, VoIP, tura fayil da sauran fasali da yawa, Leadership ta ruwaito.
An kaddamar da mahajar a kan tirken iOS a ranar 14 ga Agusta, 2013 da kuma Android a watan Oktoba 2013.
Asali: Legit.ng