Hotunan Ziyarar Da Kwankwaso Ya Kai Ondo Don Jaje Kan Kisar Masu Ibada 40 a Coci
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya kai ziyarar ta'aziyya a Owo
- Kimanin makonni biyu da suka shude ne wasu yan ta'adda suka kutsa wani coci suka halaka fiye da mutane 40 da ke Ibada a cocin
- Kwankwaso ya jajantawa mutanen Jihar Ondo ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara zage damtse don samar da tsaro a kasar
Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Senator Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyarar ta'aziyya ga mutanen Jihar Ondo kan harin ta'addanci na Cocin St Francis.
Fiye da masu ibada 40 ne aka kashe yayin da yan ta'adda suka kai hari a cocin kimanin makonni biyu da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso, yayin ziyarar ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara dage wa wurin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin yan Najeriya da masu zama a kasar, ya kara da cewa kamata ya yi tsaro ya zama gaba da komai.
Da ya ke magana a fadar Prince Ajibade Gbadegesin Ogunoye, Olowo na Owo da fadar Ojomo na Ijebu, tsohon ministan tsaron ya yaba wa gwamnan jihar kan matakin da ya dauka na inganta tsaro.
Wata sanarwa da hadimin dan takarar shugaban kasar na bangaren watsa labarai, Saifullahi Hassan, ya fitar ta ce Kwankwaso kuma ya ziyarci wurin da harin ya faru ya kuma jajantawa mutane.
Yayin da ya ke addu'ar ganin zaman lafiya ya dawo kasar, Kwankwaso ya yi addu'a ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba
A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.
Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.
Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.
Asali: Legit.ng