Halin da ake ciki yanzu sai mun ci bashi muke iya biyan albashin ma'aikata: Sabon Akanta Janar

Halin da ake ciki yanzu sai mun ci bashi muke iya biyan albashin ma'aikata: Sabon Akanta Janar

  • Da yiwuwan gwamnati ta gaza biyan kudin ma'aikata saboda yawan bashin da yayi mata katutu
  • A yanzu dai, kowace wata sai an ci bashi kafin a iya biyan kudin albashin ma'aikatan gwamnati
  • Asusun lamunin duniya ya ce idan ba'a dau mataki ba nan gaba dukka kudin shigar Najeriya bashi za'a biya da su

Abuja - Mukaddashin Akanta-Janar na tarayya, Anamekwe Nwabuoku, bayyana cewa halin da Najeriya ke ciki yanzu sai an ci bashi kan a iya biyan kudin albashin ma'aikatan gwamnati.

Anamekwe Nwabuoku ya bayyana hakan ne a taron da aka shiryawa yan kwamitin tattalin kudi a birnin tarayya Abuja ranar Talata, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa adadin kudin da gwamnati ke kashewa yanzu ya yi tashin gwauron zabo sakamakon matsalar tsaro da bukatar taimakawa al'umma.

Yace:

"Sai mun karbi bashi kafin mu iya biyan albashin ma'aikata. Wannan na nuna irin halin kuncin da muke ciki. Kudin shigar gwamnati na fuskantar kalubale."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda: Ƙarawa Dogaran Osinbajo da Aisha Buhari Girma ya Tada ƙura

"Lissafinmu ya nuna cewa sakamakon rashin kudin shiga, baitul mali ta koma neman bashi domin biyan albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Adadin kudin da gwamnati ke kashewa na kara yawa sakamakon matsin tsaro da bukatar al'umma."

Mukaddashin Akanta Janar ya bada shawarar yadda za'a shawo kan wannan lamari ta hanyar tattalin kudi, fadada hanyoyin samun kudi, toshe hanyoyin sata da fitar da kayayyki waje, riwayar TheCable.

Mukaddashin Akanta Janar
Halin da ake ciki yanzu sai mun ci bashi muke iya biyan albashin ma'aikata: Sabon Akanta Janar Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Nan da 2026, Gaba daya kudin shigan Najeriya bashi za'a rika biya da su: Asusun Lamunin Duniya

Asusun lamunin duniya watau The International Monetary Fund (IMF) ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Najeriya bashi zata rika biya da kudin shiganta gaba daya.

Wakilin IMF dake Najeriya, Ari Aisen, ya bayyana hakan ranar Litnin yayin gabatar da bayanan tattalin arzikin yankin Sahara a birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Sake Zuwa Kotu Da Kayan 'Bokaye'

Ya ce yanzu haka kashi 89% na kudin shigan Najeriya basussuka ake biya da su.

IMF ya kara da cewa kawo karshen shekarar nan ta 2022, kudin tallafin mai da gwamnati za ta rika biya zai iya kaiwa N6 trillion.

Tsakanin Junairu da Afrilu 2022, Najeriya ta biya N947.53 billion matsayin tallafin kudin mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel