ASUU ta garzaya kotu, ta maka Gwamnati sukutum a gaban Alkali a kan sha’anin yajin-aiki

ASUU ta garzaya kotu, ta maka Gwamnati sukutum a gaban Alkali a kan sha’anin yajin-aiki

  • Kungiyar Malaman Jami’a na reshen jihar Edo za su yi shari’a da Gwamnatin Godwin Obaseki
  • Lauyoyin ASUU sun kai karar Gwamnatin Edo saboda ta dakatar da ayyukanta a makarantu
  • ASUU tace Gwamna bai isa ya dakatar da su, ya hana su albashi, kuma ya kore su daga aiki ba

Edo - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta kai karar Gwamna Godwin Obaseki a gaban kotu saboda ya dakatar da ayyukanta a manyan makarantu.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni 2022, ta ce an kai Gwamnan jihar Edo kara ne a kotun ma’aikata na kasa da ke Benin.

‘Yan reshen kungiyar ASUU na jami’ar Ambrose Alli ne suka kai karar Godwin Obaseki gaban babban kotun, su na kalubalantar matakan gwamnati.

Kara karanta wannan

Lai: FG Ta Matukar Damuwa Da Yajin Aikin ASUU, Muna Aiki Kan Shawo Kan Shi

Malaman jami’ar sun ce dakatar da aikinsu da Gwamna ya yi, ya sabawa doka, kuma ya ci karo da kundin tsarin mulki, don haka aka nemi dole a janye ta.

An rahoto kungiyar ASUU ta na cewa Gwamnatin Obaseki ta yi abin da ya fi karfin hurumin ikonta.

An hada da Gwamnati da AG

Sauran wadanda lauyoyin da suka tsayawa ASUU a kotu su ke kara sun hada da gwamnatin jihar Edo da kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daliban Jami'a
Daliban Jami'ar Ambrose Alli a Ekpoma Hoto: africaforafrica.org
Asali: UGC

Bayan kungiyar ASUU ta shiga yajin-aiki, sai gwamnatin Edo ta bakin SSG watau Osarodion Ogie, ta bada sanarwar dakatar da ayyukan kungiyar a jihar.

Kamar yadda Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana, an bada umarni a daina biyan malaman jami’ar albashi saboda sun kauracewa wuraren aikinsu.

Abin har ya kai Ogie yana cewa wadanda suka tafi yajin-aikin sun rasa ayyukansu, ya kuma bada sanarwar ana neman wadanda za su iya cike gurabensu.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

A dalilin haka ne ASUU ta nemi Alkalan babban kotun da ke raba sabanin ma’aikata na kasar nan da ke zama a garin Benin su raba masu wannan gardama.

Rahoton Business Day ya nuna har yanzu ba a sa ranar da za a fara sauraron wannan shari’a ba.

Atiku ya bayyana manufofinsa

Labari ya zo maku cewa Atiku Abubakar yana maganar saida kamfanin wuta, matatun mai da jirgin kasan Najeriya idan ya karbi mulki a jam'iyyar PDP.

Alhaji Atiku Abubakar bai goyon bayan gwamnati ta rika kula da kadarorin da ke jawo mata asara. Don haka ne zai damka su a hannun 'yan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng