Dubun wani mutumi da ake zargi da haɗa bama-bamai a arewacin Najeriya ta cika
- Jami'an hukumar 'yan sanda ta ƙasa reshen jihar Taraba sun samu nasarar kama wani mutumi da ake zargi da haɗa bama- bamai a arewa
- Bayanai sun nuna cewa an samu kayayyakin haɗa bam a gidansa da makamai, ana zargin da gidan yake amfani a matsayin ma'aikata
- Kakakin yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da lamarin kama mutumin, wanda rahoto ya ce ɗan asalin jihar Zamfara ne
Taraba -Rundunar yan sanda reshen jihar Taraba da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ta kama wani mutumi da take zargi da haɗa bama-bamai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutumin ya shiga hannu ne a garin Tella da ke yankin ƙaramar hukumar Gassol a jihar Taraba ranar Laraba.
Insha Allahu zamu kubutar da duk mutanen da aka sace, da yuwuwar mu sake rufe layukan waya, Gwamnan Arewa
Rahoto ya nuna cewa yan sanda sun samu kayan haɗa bama-bamai da dama a gidan wanda ake zargin, kuma ana tsammanin yana amfani da gidan a matsayin ma'aikatarsa.
Bayan haka hukumar yan sanda ta gano manyan makamai da suka haɗa da bindigu da alburusai a hannun mutumin da ta kama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutumin da ya shiga hannu, wanda bayanai suka nuna ɗan asalin jihar Zamfara ne, ya na tsare yanzu haka a hedkwatar yan sanda reshen Taraba da ke Jalingo, babban birnin jihar.
Idan baku manta ba a kwanakin da suka gabata cikin watan da ya shuɗe, jihar Taraba ta sha fama da hare-haren ta da bama-bamai.
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Kakakin hukumar yan sanda ta ƙasa reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da batun damƙe wanda ake zargi da haɗa bama -bamai a jihar.
Sai dai mai magana da yawun 'yan sandan bai ba da cikakkken bayani kan mutumin ba da kuma matakin da suke ɗauka kan lamarin bayan nasarar cafke shi.
A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai kazamin hari kan mutane a kauyen jihar Neja, sun aika mummunar ɓarna
Wasu tsagerun yan bindiga sun kai sabon kazamin hari jihar Neja, sun kashe aƙalla mutum uku kuma sun sace wasu sama da 30.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun kwashe tsayin lokaci suna aikata ta'adi kan mutane, sun kona gidaje a harin na kauyen Garin Gidigore.
Asali: Legit.ng