Bauchi: Mummunan Gobara Ta Lakume Shaguna 42 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa
- Kimanin shaguna guda 42 ne suka kone sakamakon wata gobara da ta tashi a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa a Bauchi
- Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne daga wani shago da ake kyautata zaton matsalar wutan lantarki ya tada wutan
- Shagunan da gobarar ta shafa sun hada da shagunan aski, shagunan masu aiki da kwamfuta da shagunan masu sayar da kayan masarufi
Jihar Bauchi - A kalla shaguna 42 ne suka kone a Student Centre, ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, sakamakon gobara da ta yi sanadin asarar dukiyoyin miliyoyin naira.
Shagunan da suka kone a Block D suna bayan dakin kwanan dalibai mata ne a Yelwa Campus na jami'ar kamar yadda The Punch ta rahoto.
Shagunan da gobarar ta yi wa barna sun hada da shagunan kwamfuta, shagunan aski a shagunan sayar da kayan masarufi.
An rahoto cewa matsalar wutar lantarki ne ya yi sanadin gobarar da ta fara ci daga wani shago guda daya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.
An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.
Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.
Asali: Legit.ng