‘Yan bindigan da suka sace mutane 29 da suka je bikin aure sun nemi a kawo N145m
- ‘Yan bindiga sun tare wasu motoci a hanya a makon da ya wuce, suka dauke mahalarta daurin aure
- Yanzu ‘yan bindigan sun tuntubi abokan kasuwancin matasan da suka yi gaba da su, sun nemi miliyoyi
- ‘Yan bindigan sun lafta fansar N145m, sun ce sai an biya N5m a kan kowane mutum sannan zai kubuta
Sokoto – Miyagun ‘yan bindigan da suka dauke wasu mutane 29 da suka halarci taron daurin aure a ranar Asabar a garin Sokoto sun lafta kudin fansa.
Premium Times ta rahoto cewa ‘yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 145 kafin mutane nan 29 da suka shigo hannsu, su iya komawa gidajensu.
Mafi yawan wadanda ‘yan bindigan suka dauke, su na saida wayoyi ne a kasuwar wayar salula na Bebeji Communication Market a Gusau, jihar Zamfara.
Sakatare-Janar na kungiyar masu saida waya a kasuwar, Nasiru Musa, ya shaidawa TVC haka.
'Yan bindiga sun kira waya
A cewar Nasiru Musa, ‘yan bindigan sun tuntube su a waya a farkon makon nan. Wadannan miyagu sun lafta fansar N5m ne a kan kowane mutumi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“’Yan bindigan sun kira waya sau biyu a ranar Litinin, su na kara jaddada mana maganarsu cewa mutanenmu su na hannunsu.”
“Sun ce mu biya Naira miliyan a kan kowane mutum a cikin su 29 da ke hannunsu. Gaba daya suna neman N145m kenan.”
- Nasiru Musa
A lokacin da ‘yan bindigan suka kai hari, mutane kusan 50 aka yi tunanin cewa an yi gaba da su.
Daga baya an samu labarin wasu da aka dauke sun dawo gida, sannan ‘yan banga da ke aikin sa-kai sun yi nasarar ceto wasu mutane bakwai daga mahalartam.
Shugaban kungiyar masu harkar wayan a kasuwar da ke jihar Zamfara, Mustapha Khalifa ya shaidawa Premium Times cewa wasunsu su na jinya a asibiti.
A cewar Mustapha Khalifa, wadanda suka kubuta su na kwance a babban asibitin Talata Mafara.
N145m ya dawo N60m
Daga baya an samu rahoto cewa 'yan bindiga sun rage kudin zuwa Naira miliyan 60. Kusan duka wadanda aka dauke dai matasa ne 'yan shekara 20 zuwa 40.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bakin wani Hadimin Gwamna, Ibrahim Zauma, tayi alkawarin za ta ceto wadannan matasa daga hannun wadanda suka dauke su.
Independent ta ce an tare motocin mutanen ne a garin Dogon Awo, jim kadan bayan an bar kauyen Bimasa a karamar hukumar Tureta da ke jihar Sokoto.
Asali: Legit.ng