Yan Bindigan Da Suka Sace Shugaban CAN a Plateau Sun Bayyana Kudin Da Za A Biya Don Fansarsa
- Yan bindiga da suka sace shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar Jos ta Gabas, Rabaran James Angware sun nemi kudin fansa
- Wani na kusa da malamin addinin kiristan da aka sace ya tabbatar da hakan yana mai cewa wadanda suka sace shi sun nemi a biya N50m don fansarsa
- Mai magana da yawun yan sandan Jihar Plateau, Alabo Alfred ya ce tuni jami'ansu sun bazama don ganin sun ceto Rabaran Fadan tare da kama wadanda suka sace shi
Wadanda suka sace shugaban kungiyar kirista ta Najeriya, CAN, a karamar hukumar Jos ta Gabas a Jihar Plateau, Rabaran James Angware, sun nemi a biya N50m kafin su sako shi, The Nation ta rahoto.
An sace limamin cocin na Katolika na St Anthony a ranar Lahadi a garin Angware.
Yan bindigan sun afka gidansa, suka rika harbe-harbe kafin suka tsere da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya na kusa da malamin addinin kiristan da aka sace ta tabbatar cewa yan bindigan sun turo sako sun kuma nemi a biya Naira miliyan 50 don fansarsa.
Mai magana da yawun yan sandan Jihar Plateau, Alabo Alfred ya ce rundunar ta san da afkuwar lamarin.
"Tuni jami'an mu sun fara aiki don tabbatar da cewa Rabaran Fada ya samu yancinsa, kuma an kama wadanda ke da hannu a sace shi," in ji shi.
Legit Hausa ta samu ji ta bakin wata ma'aikaciyar cocin katolika a bangaren masu wakokin yabo wato 'choir' wacce ta bukaci a boye sunanta saboda dalilan tsaro game da hare-haren da yan bindiga ke kaiwa coci-coci musamman na katolika.
Ta ce abin bakin ciki ne da damuwa sai dai suna addu'a ga Ubangiji ya magance matsalar tsaro ba ga coci kadai ba har kasa baki daya.
Ta kara da cewa akwai alamun an fi kai wa cocin katolika hari ne domin suna da yawa kuma an san su kafaffen coci ne cikin na farko a kasar.
"Muna bakin cikin yadda ake kai wa yan uwan mu da ba su ji ba basu gani ba hare-hare a coci.
"Muna cikin addu'a a koda yaushe kuma muna fatan Ubangiji zai mana maganin lamarin," in ji ta.
ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC
A wani rahoton, Kwamitin Koli Ta Tsaro a Najeriya, NSC, ta ce Kungiyar Ta'addanci Ta ISWAP ce ta kai harin da aka kai a cocin St Francis da ke Owo, wanda ya yi sanadin rasuwar mutane 38 a ranar 5 ga watan Yunin 2022, Channels TV ta rahoto.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai na gidan gwamnati jawabi bayan taron Kwamitin Kolin Tsaro a Abuja.
Ya bayyana cewa an umurci jami'an tsaro, musamman yan sanda su kama wadanda suka aikata laifin.
Tsohon gwamnan na Jihar Osun ya ce harin ba ta da alaka da addini ko kabilanci, yana mai tabbatar da cewa hare-haren kungiyar ba ta da alaka da addini.
Asali: Legit.ng