Gwarzo: Bidiyon yadda wani Mutumi ya tuƙa Tankar man fetur da ta kama da wuta don ceton mutane

Gwarzo: Bidiyon yadda wani Mutumi ya tuƙa Tankar man fetur da ta kama da wuta don ceton mutane

  • Wani mutumi ya ja hankalin mutane bayan ya nuna rashin tsoro, ya Tuƙa Tankar Fetur da ta kama da wuta ya fitar da ita daga cikin mutane
  • Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Omo Agege, ya kira shi ta waya don jinjina masa kan kokarin da ya yi a jihar Delta
  • Mutumin wanda dama can Direba ne, ya nuna tsantsar jin daɗinsa da kiran Sanatan, ɗan takarar gwamna na APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Delta - Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Omo Agege, ya yaba wa wani direba, Ejiro Otarigho, wanda ya tuƙa Tankar Fetur da ke ci da wuta ya fitar da ita daga cikin mutane a jihar Delta.

A ƙarshen makon nan, wani Bidiyo da aka watsa a Tuwita, ya nuna yadda Otarigho ya tuƙa Tankar mai ci da wuta a ƙauyen Agbarho, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

The Cable ta ce yayin da yake zantawa da mutumin ta wayar salula, Omo-Agege, ɗan takarar gwamnan Delta na APC, ya bayyana mutumin da, "Gwarzo."

Yadda ya ceci mutane.
Gwarzo: Bidiyon yadda wani Mutumi ya tuƙa Tankar man fetur da ta kama da wuta don ceton mutane Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Sanatan ya ce ba don sadaukarwan direban ba, da wata Annobar wuta ta tashi a yankin wacce ba'a san iya ɓarnar rayukan mutane da dukiyoyin da zata yi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Aikin da ka yi ya ceci rayukan al'ummar mu waɗan da ka iya mutuwa sanadin hatsarin. Ba kowane mutum zai iya samun irin wannan karfin halin ba, abun da kayin nan ɗaya ya tseratar da Agbarho, muna alfahari da kai."
"A wurina ka zama gwarzon mutanen mu kuma ina da tabbacin mutane da yawa zasu neme ka yanzu, dan haka lokacin ka ne da zaka ji kai gwarzo ne, ina alfahari da kai."

Kara karanta wannan

EFCC Ta Sako Hadimin Zulum Da Ta Kama Kan Wallafa a Facebook Game Da Damfarar Akanta Janar

Yadda mutumin ya ji bayan kiran Sanatan

A ɓangarensa, Otarigho, ya bayyana cewa kiran da Omo-Agege ya masa ya tabbatar da yanda yake kula da nuna sanayya ga mutane.

"Mutum kamar mataimakin shugaban majalisar Dattawa ya kira ni a irin lokacin nan, na yi matuƙar farin ciki da hakan. Jin ta bakinsa ya nuna yadda yake nuna sanayya ga mutane."
"Mutane na ƙorafin ba wanda zai kula da su, inda na bar mutane sun mutu sai dai a zo ganin gawarwaki, amma yanzu na ji daɗi mataimakin shugaban majalisa ya kira ni."

Kalli bidiyo a nan

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun jami'an tsaro a hanyar Kaduna-Abuja, an sheƙe wasu

Yan bindiga sun yi yunkurin kai hari kan matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja, amma sun kwashi kashin su a hannun jami'an tsaro.

Rundunar yan sanda reshen Kaduna ta ce dakarun haɗin guiwa na sojoji da yan sanda sun fatattaki maharan da karfin tsiya.

Kara karanta wannan

Firgici: An cafle mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262