Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun Jami'an tsaro yayin da suka farmaki hanyar Abuja-Kaduna

Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun Jami'an tsaro yayin da suka farmaki hanyar Abuja-Kaduna

  • Yan bindiga sun yi yunkurin kai hari kan matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja, amma sun kwashi kashin su a hannun jami'an tsaro
  • Rundunar yan sanda reshen Kaduna ta ce dakarun haɗin guiwa na sojoji da yan sanda sun fatattaki maharan da karfin tsiya
  • Kwamishinan yan sandan Kaduna, Yekini Ayoku, ya yi farin ciki da jajircewar dakarun, ya nemi mutane su taimaka da bayanai

Kaduna - Haɗakar rundunar jami'an tsaro sun yi nasarar daƙile harin yan bindiga a kan babbar hanyar Kaduna-Abuja ranar Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Dakarun Operation Puff Adder na hukumar yan sanda da haɗin guiwar rundunar Operation Thunder Strike na hukumar sojin Najeriya sun fatattaki yan bindigan tare da halaka ɗaya a sananniyar hanyar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun yi gaba da kusan miliyan N50m a Sakatariyar karamar hukuma

Taswirar jihar Kaduna.
Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun Jami'an tsaro yayin da suka farmaki hanyar Abuja-Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, a wata sanarwa, ya ce Dakarun tsaron sun tari yan ta'addan a yankin, inda suka yi musayar wuta.

Sakamakon haka, jami'an tsaron suka yi nasarar cin ƙarfin su, hakan ya tilasta wa maharan tsere wa cikin jeji, yayin da aka aika ɗaya zuwa barzahu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jalige ya ce:

"Yayin bincika wurin da aka yi gwabzawar, jami'ai sun gano bindiga AK-47 da Babura Tara na yan ta'adddan. Jami'an tsaro ba su gajiya ba a kokarin kare rantsuwar su ta kare rayukan matafiya da sauran masu bin hanyar."

Kwamishinan yan sandan Kaduna, Yekini Ayoku, ya nuna tsantsar jin daɗinsa bisa jajircewa da gwarzantakar jami'an tsaron.

Haka na kuma ya tabbatar musu da cewa sadaukarwan su wajen kokarin kare rayuwar al'umma ya fi ƙarfin a saka musu da wani abu.

Kara karanta wannan

Firgici: An cafle mutumin da ya tada hankalin jama'a da ikrarin Boko Haram sun shigo gari

Jama'a su taimaka mana da bayanai - CP

Kwamishinan ya ƙara da cewa yan ta'addan da aka jikkata yayin gwabzawar zasu bazama yankunan da ke yankin don neman a gyara musu raunukan su.

Bisa haka, kwamishinan ya yi kira ga al'umma su gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi, inda ya tabbatar musu za'a kawo ɗauki nan take.

A wani labarin na daban kuma Bayan kusan mako daya da shan ƙasa a zaben fidda gwani, Tsohon gwamna ya tura wa Tinubu sako kan 2023

Bayan kwanaki aƙalla biyar da shan kaye, Sanata Rochas Okorocha ya tura sakon murna ga tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu.

Sanata Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ce yana wa jagoran APC na ƙasa fatan samun nasara a babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262