Hotunan El-Rufai da Jikokinsa Suna Atisaye a Tsakar Falo Sun Kayatar da Jama'a
- Babu ko shakka idan aka ce gwamnonin Najeriya da karfinsu a jiki, akasin yadda ake ta yadawa kan cewa a ofisoshinsu kadai suke zaune ba tare da motsa jiki ba
- Yanayin tsarin motsa jikin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya nuna ba haka bane, ya karyata dukkan labaran da ake yadawa na rashin karfnsu a jiki
- An ga hotunan El-Rufai yana daga jikokinsa har su uku da kafafunsa a falo yayin da ya ke kwance a kan gadon bayansa cike da nishadi
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya tabbatar da cewa jikinsa garas yake a wasu hotuna da suka bayyana yana gwada kwarewarsa a atisaye.
Gwamna El-Rufai, a jerin hotunan da aka wallafa a Facebook, an gan shi a falo yana wasa da jikokinsa.
Wani daga cikin hadiman gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Joe Igbokwe ne ya wallafa hotunan inda ya kwatanta Gwamna El-Rufai da gwarzon iyalinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
'Yan Najeriya sun yi martani
Babu dadewa da wallafa hotunan, 'yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu. Ga wasu daga cikin tsokacin:
Akachi Bernard Nwaeze "Wannan baiwa ce da Ubangiji. Na yi sha'awarta."
Yariman Buhari Maijamaa: "Gwamna! Gwamnan mutane na kwarai?"
Albert Obazee: "Gwarzon Shugaba."
2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki
A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Juma'a, 10 ga Yuni, ya bada bayanin yadda tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya zama 'dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa, ya caccaki wadanda suke sukar tikitin takara na musulmi da kuma mataimaki musulmi inda ya kwatanta su da wadanda ba su san abinda su ke yi ba.
Tinubu ya samu kuri'u 1,271 inda ya lallasa 'yan takara 13 a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da aka kammala a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng