Sunaye: Biloniyoyin Najeriya 8 sun Samu Ribar N478.1b, Dangote Yafi Kowa Kaso Mai Tsoka

Sunaye: Biloniyoyin Najeriya 8 sun Samu Ribar N478.1b, Dangote Yafi Kowa Kaso Mai Tsoka

  • Cikakkun bayanai a kan yadda dukiyar biloniyoyin Najeriya ta tumbatsa a cikin watanin 12 na shekarar 2021 ya bayyana
  • Aliko Dangote, mutumin da yafi kowa dukiya a Afirka ya jagoranci jerin biloniyoyin yayin da ya mamaye kashi 63 na gaba daya N478.1 biliyan
  • Arzikin da aka samu wanda ya kunsa man fetur da duk wasu kayyakin amfani, sun samu nasara ne bayan narka hannun jari a kamfanoni da dama

Biloniyoyin Najeriya, wadanda su ne masu hannun jari da mamallakan wasu daga cikin kamfanonin da suka fi samun riba a kasuwancin Najeriya sun samu ribar fiye da N478.1 biliyan.

Sun samu ribar ne sanadiyyar hannayen jarin a suka narka a shekarar 2021.

Dangote ne Kan Gaba a Jerin Biloniyoyin Najeriya Yayin da Ya Samu Karin N478.1b
Dangote ne Kan Gaba a Jerin Biloniyoyin Najeriya Yayin da Ya Samu Karin N478.1b. Hoto daga nairametrics.com
Asali: UGC

Kamar yadda Nairametrics ta bayyana, biloniyoyin sun samu a kalla kashi 5 na gaba daya kasonsu.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

Aliko Dangote

Aliko Dangote, shugaban kamfanin simintin Dangote, ya jagoranci kungiyar biloniyoyin 18.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda bayanai suka nuna, Dangote ya samu ribar N301.76 biliyan a shekara daya, wanda shi ne kashi 63.1 na gaba daya N478.1 biliyan.

Hannun jari da ya naraka kai tsaye ya janyo masa ribar N552.95 miliyan, yayin da hannun jarin da yasa ta wasu hanyoyi ya jawo masa ribar N292.43 biliyan, wanda gaba daya ya zama N292.98 biliyan.

Abdulsamad Rabiu

Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne na biyu kuma mamallakin kamfanonin BUA ( abincin BUA da Siminti). Kamfaninsa ya janyo masa ribar N143.09 biliyan a shekarar 2021 a matsayin kasonsa.

Jim Ovia

Jim Ovia mai Bankin Zenith ya samu kason N15.72 biliyan a matsayin riba na hannun jarin da ya narka kai tsaye da wanda ya narka ta wasu hanyoyi a bankin a matsayin kamfani.

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Abdulsamadu Rabiu (Karami)

Abdulsamad Rabiu (karami) 'da ga gawurtaccen 'dan kasuwar nan mai kamfanin simintin BUA da abinci ya samu ribar N6.27 biliyan a cikin lokacin, wanda ya kai shi matsayin attajiri na 4 a Afirka.

Tony Elumelu

Tony Elumelu, shugaban bankin UBA, ya samu ribar N2.38 biliyan a shekarar 2021.

Sauran biloniyoyin da suka narka dukiya mai tarin yawa a 2021 sun hada da;

Mike Adenuga - N1.43 biliyan

Herbert Wigwe - N1.52 biliyan

Austin Avuru - N1.99 biliyan.

Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15

A wani labari na daban, mujallar Forbes ta saki jerin sunayen wadanda suka fi kowa dukiya a duniya, wanda takwas daga cikin goma na farko 'yan kasar Amurka ne, sai daya daga Faransa da kuma daya daga Indiya.

Har yanzu, Amurka ce ke mulkar duniya, wacce ke da biloniyoyi 735 da jimillar dukiyar $4.7 tiriliyan, duk da Elon Musk, wanda yazo na farko a jerin sunayen biloniyoyin duniya a karo na farko sama da Jeff Bezos.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel