Yadda Fastoci Suka Dinga Tatse Mahaifiyata da Sunan Magance Mata Cutar Kansa, Ɗan Dora Akunyili

Yadda Fastoci Suka Dinga Tatse Mahaifiyata da Sunan Magance Mata Cutar Kansa, Ɗan Dora Akunyili

  • Obumnaeme, 'da ga marigayiya Mrs Dora Akunyili, tsohuwar ministar labarai, ya bayyana yadda wasu fastoci suka tatse mahaifiyarsa tas da sunan za su warkar da ita daga cutar daji
  • Kamar yadda 'dan marigayiyar ya bayyana, mahaifiyar tasa ta je wurin fitattun fastocin Najeriya da dama don neman magani bayan an gano tana dauke da cutar daji a mataki na 4
  • Ta yi imani da Ubangiji zai warkar da ita yayin da tayi ta narka dukiyarta gaba daya tare da girbe duk hatsinta, wanda a ganinsa hakan ba komai bane face 'ci da addini'

Obumnaeme, 'da ga marigayiya Mrs Dora Akunyili, tsohuwar ministar labarai, ya bayyana yadda wasu fastoci suka amshi kudade daga mahaifiyarsa tare da alkawarin warkar da ita daga cutar kansa (daji).

Kara karanta wannan

Saboda budurwa: Fitaccen dan kwallon Arsenal ya tabbatar da karbar addinin Muslunci

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Chudr Jideonwo, babban daraktan ofishin kula da kwangilar jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Yadda Fastoci Suka Dinga Tatse Mahaifiyata da Sunan Magance Mata Cutar Kansa, Ɗan Dora Akunyili
Yadda Fastoci Suka Dinga Tatse Mahaifiyata da Sunan Magance Mata Cutar Kansa, Ɗan Dora Akunyili. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, mahaifiyarsa ta je wurin fitattun fastocin Najeriya da dama don neman maganin cutar kansa (daji) da aka gano tana fama da ita a mataki na 4.

Ya ce, yawancinsu sun yi amfani da damar wajen tatsar kudi daga hannunta tare da yi mata karairayi, inda ya kara da cewa abun da fastocin suka yi wa mahaifiyar sa shi ne "ci da addini."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obumnaeme ya ce, "Kawai abun da tafi cewa shi ne Ubangiji zai warkar da ni; ta karar da duk kudinta, ta girbe duk hatsin. Saboda haka nake ganin damfara ne. A Najeriya, ba ma kiran shi da laifi ko wani abu, amma naga cewa hakan ci da addini ne.

Kara karanta wannan

Nwajiuba ya bayyana dalilinsa na rashin zuwa Eagle Sqaure duk da yana takara

"Ta je wurin wani fasto a Legas na tsawon mako guda. Ta dawo tare da cewa suna bukatar a yi hoto kuma Ubangiji ya warkar da ita. Sannan na tuna lokacin da mahaifina ya ke kuka yayin da ya dauke ta zuwa hoton. Ya san za su gani. Kuma bai yi kokarin yin shuru da zancen ba; ya yi kokarin kauda hasashen.
"Amma mahaifiyata, kasan yadda mutum ke imani da "Ubangiji ya warkar dani'. Da suka yi hoton suka ga yawan kansar a gurin, ta yi girma daga bisani mahaifiyata tace ga garin ku bayan kwana uku. Kawai za ka ga mutum, yana girma fiye da mutum mai rai kullum."

'Yan bindiga sun kashe mijin marigayiya Dora Akunyili

A wani labari na daban, wani rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar Ministar Yada Labarai, Farfesa Dora Akunyili.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kashe shi a Umuoji da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra da yammacin ranar Talata, 28 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Kodayake har yanzu babu cikakken bayanai game da lamarin, wata majiya ta kusa da iyalan ta ce marigayin yana nan a taron kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Najeriya Nsukka (UNAA) inda aka karrama marigayiya Dora wasu sa’o’i kafin a kashe shi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel