EFCC ta Ayyana Neman Fitaccen Fasto da Matarsa Kan Damfarar N2bn
- Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa na neman wani fasto da matarsa bayan sun yi sama da fadi da dukiyar jama'a mai tarin yawa
- An gano yadda Onyinmiebi (Mie Baraza) da Beatrice Bribena suka damfari mutane sama da N2 biliyan da sunan hannun jari tare musu alkawarin ribar kashi 25 a duk karshen wata
- Sai dai daga bisani suka yi batan dabo, wanda hakan ya tilasta mutane yin zanga-zanga bayan faston da matarsa sun gaza biyansu hakkinsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa na neman wasu ma'aurata, Onyimmiebi (Miebi Baraza) da Beatrice Bribena ruwa a jallo.
A wata takarda da kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ya rattaba hannu, EFCC tana neman ma'auratan ne ruwa a jallo bisa zarginsu da damfarar 'yan Najeriya N2 biliyan, Punch ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Adireshinsu na karshe da aka sani shi ne lamba 163 layin Mbiama Yenagoa na Biogbolo da ke jihar Bayelsa.
"Duk wanda ke da wani bayani mai amfani game da duriyarsu ya taimaka ya tuntubi hukumar a ofishinta na Benin, Kaduna, Ibadan, Sakkwoto, Gombe, Maiduguri, Makurdi, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Port Harcourt, da Abuja ko ta wadanda lambobin 0990447513, 08093322644, 070263507213, 07063507245; ko adireshinta na yanar gizo: info@efcc.gov.ng ko ofishin'yan sanda mafi kusa da sauran hukumomin tsaro", sanarwar ta ce.
An ruwaito yadda Bribena, wanda fasto ne a wata sananniyar majami'a ya tsere daga Najeriya a shekarar da ta gabata bayan ya gaza biyan masu hannun jari hakkinsu.
Bayan damfarar wasu 'yan Najeriyan da faston ya yi, sun yi zanga-zanga a Yenogoa, babban birnin Bayelsa.
Daga bisani EFCC ta rufe ofishin Bribena.
"Muna sadaukarwa wajen inganta rayuwar mambobi ta hanyar bada tallafin kudi, tallafin jari, tallafin kudi ko bashi, samar da gida, tallafin karatu da sauransu," kamar yadda kamfanin ya nuna.
Sun yi alkawarin bada ribar kashi 25 cikin dari a duk karshen wata ga duk wanda ya zuba hannun jari.
Haka zalika, kamfaninsu yana da rassa a Port-Harcourt, babban birnin Ribas da sauran sassan kasar.
A watan Julin da ta gabata, Bribena sun saki bidiyon da ke karyata jita-jitar cewa lafiyarsa da kasuwancinsa na neman rushewa.
"Ku yi watsi da irin wadannan labaran. A da can ban rushe ba sai yanzu? Ban san ko wasu mutane na jin haushin cewa Baraza zai iya dawowa," a cewarsa.
EFCC suna "aikin sirri" a filin zaben fidda gwani na APC, Majiya ta tabbatar
A wani labari na daban, wata majiya mai karfi a Hukumar Yaki da Rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da cewa jami'an hukumar na aikin sirri wurin lura da deliget tare da kiyaye yadda ake siyan kuri'u a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki.
Hajji 2022: NAHCON Ta Bayyana Kudaden Kujerun Hajjin Bana, Jihohin Borno Da Adamawa Sun Samu Rangwame
Majiyar abin dogaro, wacce ta yi magana da Punch kan a boye sunanta, ta ce, "A halin yanzu muna filin zaben fidda gwani a sirrance. Muna lura kuma muna kallon yadda ake cusawa deliget ra'ayi, ake siyan kuri'u da sauran magudin zabe na kudi da ka iya faruwa."
Asali: Legit.ng