Yanzu-Yanzu: Shugaban ASUU Ya Ƙi Karbar Tallafin N50m Daga Ahmed Isah Don Janye Yajin Aiki
- Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ya ki karbar tallafin Naira miliyan 50 daga hannun Ahmed Isah mai gabatar da shirye-shirye
- Tun a kwanakin baya ne mai gabatar da shirye-shirye a rediyo kuma mai rajin kare hakkin bil adama ya kaddamar da neman tallafin kudi domin a bawa malaman makarantar su janye yajin aiki
- A ranar Asabar, a yayin da Ahmed ya gayyaci Farfesa Osodeke a shirin Berekete Family don ya yi wa yan Najeriya bayanin dalilin yajin aikin, ya gabatar masa da N50m amma bai karba ba
FCT, Abuja - Wani abu mai kama da dirama ya faru a lokacin da kungiyar malaman jami'o'i na Najeriya, ASUU ta ki karbar kudin da Berekete Family Radio ta bata don janye yakin aiki, rahoton Daily Trust.
ASUU ta fara yajin aiki ne tun watan Fabrairu kuma kawo yanzu duk wani yunkuri da aka yi na ganin malaman sun koma aji bai yi wu ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A safiyar ranar Asabar, mai gabatar da shirye-shirye a rediyo, Ahmad Isah, da aka fi sani da Ordinary President ya gayyaci shugaban ASUU don yi wa yan Najeriya bayani kan matsalolin da suke fuskanta da dalilin da yasa ba su janye yajin aikin ba.
Isah ya kuma kaddamar da neman taimako na kudi a asusun TAJ Bank don tara kudin da za a bawa ASUU su janye yajin aiki.
A wani yunkuri na shawo kan ASUU ta janye yajin aikin ta hanyar tallafa musu da kudi, Isah ya nuna Naira Miliyan 50 da Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom ya bada a matsayin gudun mawa.
Farfesa Osodoke ya ki karbar N50m din, ya ce kada a danganta ASUU da kudin
Nan take bayan Isah ya fito da kudin, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya nuna rashin jin dadin sa ya ce kada a danganta kungiyar da wannan kudin.
A wannan matakin, Isah ya yi barazanar cewa zai dakatar da karbar tallafin kudin da ya fara don tara wa ASUU, kuma yan Najeriya da dama da suka kira waya a shirin sun ce abin da shugaban na ASUU ya yi bai dace ba.
Yajin Aiki: Fitaccen Mai Gabatar Da Shirye-Shirye a Rediyo Zai Tara Wa ASUU N18bn Don Su Koma Aji
Tunda farko, Fitaccen mai rajin kare hakkin bil adama, kuma mai gabatar da shirye-shirye, Ahmed Isah, da aka fi sani da Ordinary President ya kaddamar da kamfen don tara wa kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, Naira Biliyan 18 don su koma aji.
Isah ya kaddamar da kamfen din neman tallafin ne ga ASUU a shirin Berekete Family na musamman da aka sadaukar saboda yajin aikin ASUU kamar yadda Legit.ng Hausa ta gano ya kuma wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya jadadda cewa ba dole sai Najeriya ta ciyo bashi ba daga kasashen ketare, yana mai cewa kasar tana da kudin da za ta iya kula da kanta.
Asali: Legit.ng