Bamu yarda Musulmi da Musulmi su zama Shugaba da mataimaki ba: Kungiyar CAN
- Ba zamu taba yarda Tinubu ko Atiku su zabi Musulmi matsayin mataimakansu ba, kungiyar CAN
- Uwar kungiyar mabiya addinin Kiristan tace ko yanzu da ake shinkafa da wake suna shan wahala ina ga mulki ya koma hannun Musulmai gaba daya
- Hukumar zabe INEC ta baiwa Tinubu da Atiku mako guda su mika sunayen abokan tafiyarsu
Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta gargadi jam'iyyun siyasa kada suyi kuskuren zaben Musulmi da Musulmi matsayin yan takaran Shugaban kasa da mataimaki a 2023.
Sakataren kasan na kungiyar, Joseph Bade Daramola, ya bayyana hakan ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja, rahoton DailyTrust
A cewarsa, hakan na da hadari ga zaman lafiya da hadin kan yan Najeriya.
Yace:
"CAN na kira ga yin daidaito tsakanin addinai biyu wajen zaben abokan tafiyan yan takara kujerar shugaban kasa. Bamu yarda Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista ba."
"Duk jam'iyyar da tayi kokarin haka za ta sha kashi. Yanzu ba 1993 bane. Ko yanzu da Musulmi/Kirista ke mulki Kiristoci na shan bakar wahala."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ya abin zai kasance idan Musulmai sukayi kane-kane kan mulki? Gargadi muke yi kuma zamu dau mataki idan ba'a dauki gargadinmu ba."
Ya yi kira ga Tinubu ya dauki mataimaki daga Arewa, Atiku ya dau Kirista daga kudu kuma Peter Obi ya dau Musulmi daga Arewa.
Ba zamu yarda Tinubu ya dauki Musulmi matsayin abokin tafiyarsa ba, Babachir Lawal
Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa ba zai yiwu Tinubu ya dauki wani Musulmi matsayin mataimakinsa ba a zaben 2023.
Babachir ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Seun Okinbaloye na ChannelsTV.
Ya ce sam ba zai yiwu wani yayi tunanin tikitin Musulmi da Musulmi ba dubi ga yadda lamarin siyasar Najeriya yake.
Babachir yace akwai bukatar jam'iyyar tayi nazari da kyau kafin zaben wanda zai yiwa Tinubu mataimaki.
Asali: Legit.ng